Tarayyar Turai ta ki goyon bayan Amurka a yakin Iran
March 19, 2026
A cikin jawabin da ya gabatar a gaban majalisar dokokin Jamus Bundestag, shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz ya ce ba a tuntubi Jamus ba kafin fara wannan yakin, yana mai cewa da an nemi ra'ayinsu, da sun nuna adawa da wannan hakan.
Haka kuma, Shugaban gwamnatin na Jamus ya jaddada cewa kasarsa ba za ta shiga cikin duk wani matakin soja da ya shafi bude mashigin ruwa na Hormuz ba.
Wannan furuci na Merz ya zo ne bayan ministan tsaron kasar, Boris Pistorius, ya bayyana a ranar Litinin cewa Jamus ba ita ta fara wannan yaki ba, don haka ba za ta shiga ba.
A daya bangaren kuma, shugabannin kasashen Turai sun ki shiga kai tsaye cikin hare-haren da Isra'ila da Amurka ke kai wa Iran, saboda fargabar fadawa cikin rikici mai sarkakiya wanda makomarsa ba ta bayyana ba, kuma wanda al'umomin kasashensu ba su goyon bayansa.