1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya jadadda matsayinsa na neman mallakar Greenland

Mouhamadou Awal Balarabe
January 21, 2026

A yayin da yake jawabi a taron tsara manufofin tattalin arziki na duniya a Davos, Trump ya yi kira da a gudanar da taro cikin gaggawa kan niyyar kasarsa ta mayar da yankin Greenland karkashin ikonta.

https://p.dw.com/p/57CX5
Shugaba Donald Trump da shugaban taron Davos Borge Brende a yayin tattaunawa
Shugaba Donald Trump da shugaban taron Davos Borge Brende a yayin tattaunawaHoto: Jonathan Ernst/REUTERS

Shugaba Donald Trump na Amirka ya yi ikirarin cewar kasarsa ce kadai a duniya ke da karfin tabbatar da tsaron yankin Greenland na Denmark, yana mai cewa babu wata mamba ta kungiyar tsaro ta NATO da za ta iya kare tsibirin yadda ya kamata.

A yayin da yake jawabi a taron tsara manufofin tattalin arziki na duniya a Davos, Trump ya yi kira da a gudanar da taro cikin gaggawa kan niyyar kasarsa ta mayar da yankin Greenland karkashin ikonsa. Sai dai  Denmark wacce memba ce a kungiyar tsaro ta NATO ta soki wannan matsayi saboda Greenland wani bangare ne na  kasar. 

Karin bayani: Wai shin taron Davos zai magance rikice-rikicen duniya?

Shugaba Trump na Amurka, wanda shugabannin Turai suke suka, ya kai mayar musu da martani yana mai cewa nahiyar ba ta karfin tafiyar da Greenland yadda ya kamata. Trump ya ce: "Ina girmama mutanen Greenland da 'yan Denmark sosai. Amma kowace kasa da ke da kujera a NATO na da alhakin kare kanta, amma gaskiyar magana ita ce, babu wata kasa ko kungiyar da ta iya kare Greenland sai Amurka. Kasa ce mai karfi kuma muna da karfi fiye da yadda mutane suka zato."