1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya nuna alamar samun maslaha a Gabas ta Tsakiya

September 28, 2025

A wani sako da ya wallafa a shafin Truth Social, Trump ya ce "wani abu na musamman na shirin faruwa a Gabas ta Tsakiya".

https://p.dw.com/p/51CS7
Amurka na daga cikin kasashen da ke shiga tsakani a yakin da ake yi a Gaza.
Amurka na daga cikin kasashen da ke shiga tsakani a yakin da ake yi a Gaza.Hoto: POU/ROPI/picture alliance

Shugaban Amurka Donald Trump ya nuna alamar samun maslaha a rikicin Gabas ta Tsakiya, inda ya ce "ana cikin shiri don yin wani abu na musamman,” a daidai lokacin da Firaministan Israila Benjamin Netanyahu zai kai ziyara Fadar White House.

Trump ya ce akwai cikakkiyar dama ga nasara a Gabas ta Tsakiya a wani sako da ya wallafa a shafinsa na Truth Social.

Amurka ta gabatar da sabon shiri kan Gaza

Tun a ranar Juma'a, Trump ya shaida wa manema labarai a Washington cewa ya na ganin an samu yarjejeniya kan Gaza.

Ganawar da ake sa ran za ta wakana tsakanin Netanyahu da Trump a Fadar White House a ranar Litinin na zuwa ne kwanaki bayan shugaban na Amurka ya gabatar da wani shiri mai matakai 21 da nufin kawo karshen yaki a yankin Falasdinawa.

Trump ya goyi bayan Isra'ila bayan sukar Rasha a taron MDD

Har ila yau, shugaban na Amurka ya gabatar da shirin ne lokacin da yake tattaunawa da shugabannin kasashen Larabawa da na Musulmi a gefen babban taron Majalisar Dinkin Duniya.