1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump: Za mu iya daina kai hari Iran nan da makonni 2-3

April 1, 2026

Trump ya ce farmakin Amurka da Isra’ila kan Iran na iya karewa cikin makonni 2–3, yana mai cewa kasashen duniya su dauki alhakin bude Mashigar Hormuz, yayin da farashin mai ke kara tashi.

https://p.dw.com/p/5BW4t

Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana cewa Amurka za ta janye hannu daga kula da mashigar Hormuz, inda ya ce kasashen da ke dogaro da ita wajen samun man fetur da harkokin jiragen ruwa su dauki alhakin bude ta.

Trump ya nuna rashin jin dadinsa da kawayen Amurka da ba su bayar da isasshen goyon baya ba, inda ya ce su "nemo man nasu da kansu.”

Karin bayani: Iran na shirye ta dakatar da yaki amman da sharadi

A bangaren Iran kuwa, ministan harkokin wajen kasar Abbas Araghchi ya tabbatar da karbar sakonni daga wakilin Amurka, amma ya ce babu wata tattaunawa, yana mai cewa babu aminci a tsakaninsu da Amurka .

Haka kuma sabon jagoran addinin Iran Mojtaba Khamenei ya sha alwashin ci gaba da goyon bayan kungiyoyin da ke adawa da Isra'ila a yankin Gabas ta Tsakiya.

Yakinna ci gaba da shafar tattalin arzikin duniya, inda farashin mai a Amurka ya haura dala hudu a kan kowane galan karo na farko tun 2022, lamarin da masana ke cewa zai iya kara tashin farashin abinci.