1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tura sojin Najeriya zuwa Benin ya bar baya da kura

December 8, 2025

Duk da cewar an yi nasarar murkushe masu ikrarin juyin mulki, amma matakin gwamnatin Najeriya ta dauka na tura sojojinta zuwa kasar Benin na haddasa cece-kuce.

https://p.dw.com/p/54yeP
Benin Cotonou 2024 | Patrice Talon, Präsident von Benin, in Cotonou
Patrice TalonHoto: Ute Grabowsky/photothek/IMAGO

 Wasu jiragen yakin tarayyar Najeriar da sojoji na kasa ne suka taka rawa mai  tasiri wajen murkushe juyin mulkin. Sai dai a karkashi kundin tsarin mulkinta, ana bukatar amincewar majalisun kasar guda biyu kafin tura sojan kasar zuwa kasashen waje.

A kokari ceton tsarin dimukuradiyyar Benin, wasu jiragen yakin tarayyar Najeriyar guda biyu suka rika jefa bam a barikokin Cotonou, ko bayan tura sojoji na kasa zuwa cikin birnin da nufin dakile juyin mulkin da ke zaman barazana a dimukuradiyyar kasashen ECOWAS. Sai dai kuma jingine ka'ida a bangaren Najeriyar, da kila gaggawar da ke cikin tsomin bakin na jawo kace nace cikin kasar a halin yanzu.

Benin Cotonou 2025 | Soldaten verkünden Putschversuch im staatlichen Fernsehen
Masu ikirarin juyin mulki a BeninHoto: Benin TV/REUTERS

A baya, an zargi Abuja da kau da kai cikin  batun tsaron kasar bayan kallon kame da kila ma kashe wani hafsan sojan  da ke jagorantar yaki da ta'addan Boko Haram. Kuma ko bayan nan, tsomin bakin na Abuja na kama da baki iri biyu a bangaren tarayyar Najeriyar da ta kau da kai bisa juyin mulki a kasar Gunea Bissau inda ta jibge sojoji domin hana juyin mulki a lokaci mai nisa, amma kuma ta kau da kai bayan karbe ikon. A yayin da kuma ta sa kafa ta doke sojan da ke neman kwace mulkin Benin.

Koma ya zuwa ina Najeriyar take shirin ta kai a kokarin kare demokuradiyar kasashen ECOWAS  dai, yunkurin juyin mulkin dai na nuna irin girman barazanar da ke gaban kasashen yankin. Rashin tsaro dama gazawar mulki dai ce ake ta‘allakawa da kokarin sojojin na kai demokuradiyyar kasashen yankin ya zuwa cikin gidan tarihi. To sai dai kuma sabon salon na nunin kwanjin sojan dai a tunanin Dr Umar Ardo da ke zaman kwarrare a cikin tarihin soja, ya saba da ka'ida ta kasa da kasa.

Nigeria | Präsident Bola Tinubu
Präsident Bola TinubuHoto: Sarah Meyssonnier/AP/picture alliance.com

Matakin tarayyar Najeriyar na zuwa kasa da watanni da tsallake siradi na kasar Amurka, da ta yi barazanar kai hari a kan kasar. Amma kuma kuma sabon salon da ke a Abujar ya banbanta da barazanar Trump bisa tarayyar Najeriya.

Karuwar juyin mulki cikin kasashen ECOWAS na iya tasiri bisa makomar tarayyar Najeriyar da ke zaman daya tilo da tsarin demokuradiyarta ke zaman mai karfi.