Ukraine: Adadin wadanda harin Rasha ya kashe ya karu
November 14, 2025
Adadin wadanda suka mutu sakamakon mummunan harin da Rasha ta kai wa birnin Kiev fadar gwamnatin Ukraine a daren jiya wayewar yau ya karu zuwa mutum shida, kamar yadda sabbin alkaluman ma'aikatar cikin gida ta kasar suka nunar.
Alkaluman sun kuma nuna cewa harin da Rasha ta kai da jirage maras matuka da kuma makamai masu linzami ya yi wa gine-gine da dama illa, tare da haddasa gobara a wasu sassan Kiev.
A cikin sakon da ya wallafa a shafin Telegram, magajin garin Kiev Vitali Klitschko ya umurci mazauna birnin da su garzaya wuraren buya domin tsira da rayukansu saboda karin hare-haren da ake fargabar za su biyo baya.
Tuni dai kasashen Yamma ciki har da Jamus saka fara yin tir da wannan mummunan hari tare da bayyana Shugaba Putin a matsayin maras imani, yayin da kasar Azerbaidjan ta gayyaci jakadan Rasha da ke birnin Baku domin nuna bacin rai kan yadda hari ya shafi ofishin jakadancinta da ke Kiev.