1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Ukraine: Rasha ta kwace iko da kauyen Potapiva

March 22, 2026

Ma'aikatar tsaron Rasha ta ce dakarunta sun kwace iko da kauyen Potapiva na yankin Sumy da ke kan iyakar kasar da Ukraine.

https://p.dw.com/p/5AsvX
'Yan kwana-kwana na kokarin kashe gobara bayan harin Rasha a yankin Sumy
'Yan kwana-kwana na kokarin kashe gobara bayan harin Rasha a yankin SumyHoto: Ukrainian Emergency Service/AP Photo/dpa/picture alliance

Kawo yanzu Ukraine ba ta mayar da martani kan ikrarin Moscow ba na kwace iko da kauyen a yankin Sumy da ke kan iyakar kasashen biyu. Rasha ta yi ta kokarin ta samar da wani wuri a yankin Sumy domin ta kara nesa daga inda ake fada a tsakanin iyakar kasashen. Sai dai Ukraine ta ce tana kokarin dakatar da yunkurin na Rasha, hakan ya sanya ta kasa samun wani karfin iko a yankin.

Karin bayani: Rasha ta kwace iko da wasu kauyuka uku a gabashin Ukraine

Tun bayan kaddamar da mamaya a Ukraine a shekarar 2022, Rasha ta kwace iko na kashi daya bisa biyar na yankunan Ukraine. Sai dai a watan Fabarairun wannan shekarar, alkalumma sun yi nuni da cewa ta samu koma baya cikin shekaru biyu.