1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTarayyar Rasha

Ukraine ta kai hari kan cibiyar kera makaman Rasha

February 21, 2026

Hukumomin Rasha sun ce harin na Ukraine ya yi sanadin jikkatar mutane da dama sannan ya sa an dakatar da zirgar-zirgar jiragen sama a yankin Urdmur.

https://p.dw.com/p/59CTW
Cibiyar kera makamai a Ukraine
Cibiyar kera makamai a UkraineHoto: Efrem Lukatsky/AP Photo/picture alliance

Sojojin Ukraine sun kai hari a cibiyar wata muhimmiyar masana'antar kera makamai da ke Rasha a wannan Asabar, wadda kafafen yada labarai Rasha suka bayyana a matsayin cibiyar kera makamai masu linzami da Moscow ke tinkaho da ita.

Harin da dakarun Ukraine suka kai a yankin Urdmur da jirage maras matuka ya yi sanadin jikkatar mutane akalla 11 ciki har da wadanda suka ji munanan raunika kamar yadda ma'aikatar kiwon lafiya ta yankin ta sanar.

Sai dai jim kadan bayan harin rundunar sojin Ukraine ta ce dakarunta sun kai hari a wata cibiyar kera makamai da ke kusa da birnin Votkinsk inda suka yi amfani da makamai masu linzami sumfurin FP-5 Flamingo wadanda kasar ke kerawa.

Hukumar kula da zirga-zirgar jiragen sama ta Rasha ta ce filayen sauka da tashin jiragen sama na yankin Urdmurt sun dakatar da aiki a wannan Asabar biyo bayan wannan harin da ya yi kana da na ba zata.