Ukraine za ta gudanar da zabe duk da hali na yaki
December 10, 2025
Talla
Shugaban Ukraine, Volodymyr Zelensky, ya bayyana cewa a shirye yake ya gudanar da zabe cikin kwanaki 60 zuwa 90 duk da ci gaba da yaki da ake yi, muddin dai Amurka da Turai za su tabbatar da tsaro.
Sai dai Shugaba Zelenskyy ya ce dole ne a yi garambawul ga dokar zabe kafin hakan.
A halin yanzu, doka mai nasaba da yaki a kasar na haramta gudanar da zaben shugaban kasa, da na majalisa da ma na kananan hukumomi, kuma ba a yarda a sauya tsarin mulki yayin wannan lokaci ba.
Tun da farko, shugaban Amurka Donald Trump ya matsa wa Ukraine kan gudanar da zabe, yana zargin Shugaba Zelenskyy da rashin tafiyar da sahihin dimukuradiyya.
Gwamnatin Ukraine ta karyata wannan, tana mai cewa ikon shugaban kasa na nan daram a lokacin dokar ta-bacin yaki.