'Yan gudun hijira na fama da matsalolin sauyin yanayi
November 10, 2025
Yayin da wasu mahalarta 50,000 daga kasashen duniya sama da 190 suka fara taron sauyin yanayi na COP30 a birnin Belem na kasar Brazil.
Majalisar Dinkin Duniya ta yi kira ga taron da ya samar da kudade ga kasashe matalauta. Hukumar ta UNHCR, ta ce nan da shekaru 15 masu zuwa, yankunan da ke karbar kusan rabin ‘yan gudun hijira na duniya za su fuskanci mummunan tasirin sauyin yanayi.
Rahoton hukumar ya ce kalubalen da sauyin yanayi ke haifarwa na kara yawan bukatun jin kai da kuma hadarin da mutane ke fuskanta na zama ‘yan gudun hijira.
Kazalika rahoton ya ce zuwa tsakiyar wannan shekarar mutane miliyan 117 ne suka rasa matsugunansu sakamakon yaki da tashe-tashen hankula da kuma kauracewa gidajensu, inda uku daga cikin hudun su ke zaune a kasashen da ke fuskantar manyan bala'o'in muhalli.
Karin Bayani : Yawaitar 'yan gudun hijira daga Afirka inji UNCHR