1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Magyar ya kada Orban a zaben Hungary

April 13, 2026

Firaminstan Hungary Victor Orban ya amince da shan kaye a zaben 'yan majalisar dokokin kasar tare da taya abokin hamayyarsa Peter Magyar murnar nasara.

https://p.dw.com/p/5C4Xz
Peter Magyar, madugun adawan Hungary da la lashe zabe
Peter Magyar, madugun adawan Hungary da la lashe zabeHoto: Denes Erdos/AP Photo/picture alliance

Peter Magyar mai ra'ayin kusanci da Turai, ya lashe zaben 'yan majalisar dokokin Hungary da gagarumar nasara, inda jam'iyyarsa ta Tisza ta samu kujeru 138 cikin 199 yayin jam'iyyar Fidesz ta firaminista mai barin gado Victor Orban ta samu kujeru 55 kacal.

Orban ya bayyana sakamakon zaben na ranar Lahadi a matsayin mai radadi, sannan kuma ya taya jam'iyyar adawa ta Tisza da shugabanta Peter Magyar murnar samun nasara.

Shugabannin kasashen Turai da dama sun taya Peter Magyar murna, ciki har da shugaban Faransa Emmanuel Macron da shugaban gwamnatin Jamus Friedrich Merz da kuma firaministan Poland.

A nasa bangaren, Peter Magyar ya yi alkawarin zama mamba mai biyayya ga Tarayyar Turai, duk da cewa kamar wanda zai gada Orban, shi ma bai goyi bayan aika makamai zuwa ga Ukraine ba.

JD Vance na ziyara a Hungary gabanin zaben kasar

Wannan kaye da mista Orban ya sha ya zama abin kunya ga shugaban Amurka Donald Trump, wanda ya aike da tawaga ta musamman zuwa Hungary ana tsaka da yakin neman zabe domin karfafawa firamintan mai barin gado gwiwa.