Najeriya: Wace jam'iyya Kwankwaso zai shiga?
March 23, 2026
Zuwa yanzu dai mabiya jam'iyyun adawa na ta zagaraftu a gidan Kwankwasiyya da ke Miller Road, domin ganin sun janye madugun akidar ta Kwankwasiyya Dakta Rabi'u Musa Kwankwaso. Bikin kalankuwar sallah da aka saba yi duk shekara a gidan madugun Kwanwkasiyyar da ke Miller Road a Kano, ya bude wani shafi a siyasar gidan.
An dai yi arba da jiga-jigan jam'iyyun adawa, wadanda ke nuna kwalamar samun shigar Kwankwason cikinsu. Ga misali an ga gwamnan Oyo seyi Makinde na jamiyyar PDP tsagin Turaki, haka kuma an ga madugun sabuwar jami'iyyar NDC Serieke Dickson gefe kuma ga jigon jamiyyar ADC Peter Obi da shima ake ganin ya shiga fadar ta Miller Road ne domin rara-gefen neman hadin kan Kwankwaso.
Wannan lamarin dai, ya sa ana ganin zai iya zama wani abin tashin hankali ga jam'iyyar APC mai mulki a kasar. Sai dai mai magana da yawun jam'iyyar APC a Kano Auwal Soja ya ce, wannan hadaka ko a jikinsu wai an tsikari kakkausa. A cewarsa hadin kai ne irin na 'yan dambe an sha yi gayyar tana watsewa, har yanzu kuma ba su rufewa madugun kofar shiga jam'iyyarsu ta APC ba tun da ma can tare ake. Haka shima Mu'azzam Ibrahim Sanata ya ce, har babu na zaba a cikin wadannan zaurawa da ke wa Kwankwaso kai kawo.
To amma guda cikin manyan na hannun daman Kwankwaso tsohon kwmaishinan da ya ajiye aiki Dakta Yusuf Ibrahim Kofar Mata ya ce, wannan hadaka tafiya ce mikakkiya ta kokarin ceto Najeriya. Har yanzu dai ba a jiyo komai daga bakin madugun ba a kan wannan yanayi, sai dai kowa ya baza kunne da nufin jin abin da zai fada dangane da tarin masu zawarcin nasa.