Ina aka dosa a taron sauyin yanayi?
November 10, 2025
Tsakanin mutane 40,000 zuwa 50,000 ciki har da shugabannin kasashe da gwamnatoci daga kasashe kusan 200 ne ke halartar taron sauyin yanayi na Majalisar Dinkin Duniya karo na 30, don tattauna matakan da za a dauka don ba da kariya ga yanayi.
Tasirin taron
Hasali ma dai, ana tanadi jiragen ruwa guda biyu a tashar jiragen ruwa a kusa da babban birnin Belém na arewacin Brazil, domin su zama masauki ga sama da mutane 10,000 da ke halarta COP 30 na wannan shekara. Dalili kuwa shi ne, karanci da tsadar wuraren saukar baki a Belém.
Shugaban Brazil mai masaukin kai Lula, ya danganta Cop 30 da taron tsage gaskiya, duba da yanayi da kasarsa ke ciki na karuwar gobarar daji da fari. Ko da a gandun daji Amazon da ke da matukar muhimmanci ga yanayin duniya, mutanen na fuskantar matsalar bacewar halittu da tsirrai sakamakon sare dazuzzuka, saboda haka ne Brazil ta ayyana COP30 a matsayin taron aiwatarwa.
Matsalolin da suke tarnaki
Ya zuwa yanzu dai, kasashen duniya sun kasa cimma burinsu na takaita dumamar yanayi zuwa digiri 1.5 na Celsius. A maimakon haka ma dai, hanyoyin cimma wannan burin na rufuwa daya bayan daya.
Babu wata kasa da ke fada a ji a duniya da ke yin abin da ya dace wajen iyakance dumamar yanayi zuwa digiri 1.5 na Celsius, a daidai lokacin da ake cika shekaru goma da yarjejeniyar yanayi ta Paris ta 2015.
Batutuwan da ake tattaunawa
Daya daga cikin manyan batutuwa zai kasance sajewa da sauyin yanayi, saboda ana jin tasirin a ko'ina cikin duniya musamman a fannin tattalin arziki da yanayin halittu, da rayuwar al'umma. Kasashe masu talauci da masu tasowa, wadanda sauyin yanayi ya fi shafa suna bukatar samun hanyoyin samun amfani da kimiyya da fasaha da karin tallafin kudi daga kasashe masu ci-gaban masana'antu.
Muhimmiyar tambaya da ke tasowa ita ce ko kasashen duniya za su rage hayakin da ke lalata muhalli da sauri koko a'a. Tun a watan Satumba ne aka sa rai duk kasashe za su gabatar da sabbin manufofinsu kan kare muhalli, amma a cewar Shugaban COP Andre Correa do Lago, zuwa watan Nuwamba kasashe 62 ne kawai suka gabatar da su, kuma har yanzu ba a samu sabbin manufofi daga kasashe 63 ba, ciki har da wadanda suka fito daga kungiyar EU.
Ga kasar Brazil dai, Cop30 na da matukar muhimmani, saboda tana gabatar da kanta a matsayin kasa da ke hada ci-gaba mai dorewa da ci-gaban tattalin arziki, wacce za ta iya daukar nauyin jagoranci a matakin duniya.
Abin da Brazil za ta gabatar
A farkon taron Cop 30, Brazil za ta gabatar da wani shiri na kare dazuzzukan a wurare masu zafi, wadanda suke da mahimmanci wajen daidaita yanayi da halittu. Wannan ya kunshi sabon asusu da za a kafa da kudin gwamnati da masu zuba jari masu zaman kansu, inda za a ba wa kasashen da ke ba da kariya ta musamman ga dazuzzukansu lada da ribar da aka samu daga asusun. Akalla kashi 20 cikin 100 na kudaden ne za a ware su ga kungiyoyin 'yan asalin kasashen da suka kushin dazuzzukan, inda manufar ta kasance tara jimillar dala biliyan 125 na Amurka a asusun.
Sannan za a mayar da hankali kan kungiyar Tarayyar Turai EU, saboda a baya ta kasance jagora a fannin yaki da sauyin yanayi, amma a halin yanzu akwai muhawara mai zafi game da manufar rage hayaki mai gurbata muhalli kan nan da shekara ta 2040 a nahiyar ta Turai.
Baya ma ga gasa sauke nauyin da ke kanta, Tarayyar Turai na zuwa Belém ba tare da wani sabon buri ko kuduri a fannin sauyin yanayi ba, lamarin da aka dora alhakki kan Jamus.
Ko da yake gwamnatin Jamus ta sanya burin rage dumamar yanayi kan nan da shekarar 2045, amma wannan burin ya yi hannu riga da tsare-tsaren da kasar ke aiwatar da su a halin yanzu. Hasali ma dai, tana da niyyar kara fadada ayyukanta a fannin iskar gas, sannan ba ta da niyyar kara samar da makamashin da ake sabuntawa.