1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Wani iftila'i ya kashe rayukan jama'a a kasar Kenya

November 1, 2025

Wani sabon iftila'in zaftarewar kasa a Kenya ya yi sanadiyyar salwantar rayuka tare da batar wasuda dama. Kenyar dai na fama da bala'o'i a baya-bayan nan, lamarin da ke shafar mutane da kadarorinsu.

https://p.dw.com/p/52xcB
Hoto: AFP

'Yan sanda a yammacin kasar Kenya sun tabbatar da mutuwar akalla mutane 13 sakamakon zaftarewar kasa sanadiyyar ruwan sama mai yawa.

Lamarin ya faru ne a gundumar Elgeyo Marakwet, a yankin Rift Valley.

Kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa 'yan sanda sun ce mutane 19 aka ceto su, yayin da har yanzu wasu ba a san inda suke ba.

Ma'aikatar kula da al'amuran cikin gida a Kenya, ta ce an aika jiragen sama na sojoji da 'yan sanda domin taimaka wa aikin ceto.

A ‘yan shekarun nan, irin wannan bala'in na sanadin daruruwan mutane a sassan Kenya daban-daban.

A makon nan ma, girgizar kasa a gabashin Yuganda makwabciyar Kenya ta hallaka akalla mutane 13, a cewar kungiyar agaji ta Red Cross.