Wanki ya koma ruwa a Sudan ta Kudu
February 18, 2014
Talla
An ba da rahoton cewar dakarun da ke goyon bayan tsohon mataimakin shugaban ƙasar Sudan ta Kudu Riek Machar sun kai wani hari a garin Malakal mai arzikin man fetur. Masu aiko da rahotannin sun ce ana gwabza ƙazamin faɗa tsakanin dakarun gwamnatin da na 'yan tawayen a gewayen garin da ke a yankin yammaci.
Wannan ita ce karawa ta farko da aka yi tsakanin 'yan tawayen da dakarun gwamnatin,tun lokacin da ɓangarorin biyu suka rataɓa hannu a kan wata yarjejeniyar tsaigata buɗe wuta a cikin watan Janairun da ya gabata.
Mawallafi : Abdourahamane Hassane
Edita : Saleh Umar Saleh