1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Ya ta kaya a karshen mako?

Mouhamadou Awal Balarabe LMJ
November 24, 2025

Kungiyar Rivers United ta Najeriya ta sha kashi tamkar kurar roko, a hannun Pyramids ta Masar a wasan zagayen gasar zakarun kwallon kafa na nahiyar Afirka na farko.

https://p.dw.com/p/548gS
Masar | 2025 | Al Ahly
Da ma dai kungiyoyin kwallon kafa na lig din Masar, sun saba yin fice a harkar kwalloHoto: Ahmed Awaad/NurPhoto/IMAGO

Za mu yaye kallabin shirin ne da gasar zakarun Afirka ta kwallon kafa, inda kungiyoyin da aka fi ji da su suka fara kakar wasa da kafar dama.  A wasan farko na matakin rukuni da ya gudana a karshen mako, Mamelodi Sundowns ta Afirka ta Kudu ta samu nasara a gida da ci 3-1 a kan Saint-Éloi Lupopo ta Jamhuriyar Dimukuradiyyar Kwango, yayin da Young Africans ta Tanzaniya ta lallasa AS FAR ta Maroko da ci 1-0. A nata bangaren Al Ahly ta Masar, ta yi wa JS Kabylie ta Aljeriya dukan kawo wuka 4-1.

Amma Espérance Tunis da Stade Malien ta Bamako sun yi canjaras 0-0, yayin da kungiyar Pyramids FC ta Masar ta mamaye wasan da ta yi da Rivers United ta Najeriya da ci 3-0. Ita ma RS Berkane ta Maroko ta samu nasara da ci 3-0 a kan Power Dynamos da ke zama zakaran kwallon kafar Zambiya. Ita kuwa Simba SC ta Tanzaniya da sha kashi a hannun Petro Luanda ta Angola da ci 0-1. A nata bangaren, Al Hilal ta Sudan ta lallasa MC Alger da ci 2-1.
A Kamaru, rikici ya kunno kai a fagen kwallon kafa, bayan da ministan wasannin ya dakatar da zaben shugabancin Hukumar Kwallon Kafar ta kasar da ya kamata ya gudana a ranar 29 ga wannan wata na Nuwamba. Ita dai gwamnati na zargin shugaba mai ci da kawar da duk 'yan takara da za su iya taka rawar gani a zaben, lamarin da Samuel Eto'o Fils ya danganta da katsalandan da keta dokokin FiFA. Wannan fito na fito ya haifar da cece-kuce tsakanin 'yan kasar, duba da cewa Samuel Eto'o da ya kwashe shekaru hudu a kan kujerar shugabancin Fecafoot ya yi kulle-kullen da suka ba shi damar zama dan takara daya tilo.

Kamaru | Kwallon Kafa | Samuel Eto'o
Shugaban Hukumar Kwallon Kafa ta Kamaru Samuel Eto'oHoto: LILLIAN SUWANRUMPHA/AFPGetty Images
Jamus | Bundesliga | Kwallon Kafa | FC Bayern Munich | SC Freiburg
Bayern Munich ta saba jika aiki, ga duk kungiyar kwallon kafa da ke fafatawa da itaHoto: Philippe Ruiz/picture alliance

An gudanar da mako na 11, na babban lig din kwallon kafa na Jamus wato Bundesliga. Babban abin da ya fi daukar hankali shi ne rawar da Augsburg ta taka, inda ta bi Bayern har gida ta fara zura mata kwallaye biyu a filin wasa na Allianz-Arena. Sai dai daga bisani Bayern Munich ta farka tae da zazzaga kwallaye daya bayan daya har shida. Godiya ta tabbata ga Michael Olise, a cewar kocin Bayern Vincent Kompany.

Har yanzu dai Bayern Munich na saman teburi da maki 31, yayin da RB Leipzig ke biya mata baya da maki 25 bayan da ta samu nasara a kan Bremen da ci 2-0. Ita kuwa Leverkusen ta yi abin yabo, inda ta tdawo matsayi na uku da maki 23 bayan da ta bi Wolfsburg har gida kuma ta doke ta da ci 3-1. Amma Borussia Dortmund ta kasa cire wa kanta kitse a wuta a karawar da ta yi a gida da Stuttgart, inda aka tashi 3-3 duk da cewa BvB din ce ta fara zura kwallaye biyu kafin a tafi hutun rabin lokaci.

A Ingila, abubuwa na kara dagule wa Mohamed Salah bayan da Liverpool ta sake shan kashi a gida a karshen mako a hannun Nottingham forest da ci 0-3, ta koma matsayi na 11 a teburin Premier League, matsayin da ya sa kocin Liverpool Arne Slot dan kasar Netherland rasa inda zai sa kanshi. Yanayin da Liverpool ke ciki ya haifar da guna-guni tsakanin magoya baya da masu sha'awar lig na Ingila, saboda kulob din ya kashe sama da Euro miliyan 480 a lokacin musaya da cinikin 'yan wasa na bazara da ya gabata, amma duk da haka babu wani sabon dan wasa da ya fara taka rawar gani.

Ingila | Birtaniya | 2025 | Liverpool | Kwallon Kafa
Kungiyar kwallon kafa ta Liverpool ta Ingila, na yin abin kunya a banaHoto: James Baylis/Sportimage/IMAGO

A halin yanzu dai, Arsenal ce ka saman teburin Premier League da maki 29 bayan da ta doke Tottenhem da ci 4-1. Ita kuwa Chelsea tana a matsayi na biyu da maki 23 sakamakon nasarar da ta samu a kan Burnley da ci 2-0, yayin da manchester city ke ci gaba da rike matasayinta na uku da maki 22 duk da lallasa ta da Newsastle ta yi da ci 2-1.-

A fagen tennis Italiya ta yi nasarar lashe kofin Davis na uku a jere a gaban Spain a ranar Lahadi a birnin Bologne, duk da rashin taurarinta Jannik Sinner da Lorenzo Musetti. Flavio Cobolli da ke matsayi na 22 a duniya ne ya cire wa tawagarsa ta Italiya kitse a wuta, inda ya doke Jaume Munar na Spain da 1-6, 7-6 (7/5), 7-5, 'yan sa'o'i bayan Matteo Berrettini da ke matsayi na 56 a duniya ya doke Pablo Carreno na Spain da 6-3, 6-4.

Ko da yake Italiya har yanzu ba ta kama kafar Amurka da ta lashe gasar Davis Cup sau 32 ba, amma ta yi nasara ta hudu a gasar bayan nasarorin da ta samu a 1976, 2023, da 2024. Wannan nasarar ta fi ban mamaki, domin ta cimma ta ba tare da lamba 2 a duniya Jannik Sinner ba da yake shirye-shiryen tinkarar kakar wasa ta 2026.