WFP ya dakatar da aikinsa a arewacin Yemen
January 29, 2026
Talla
Shirin samar da abinci na Majalisar Dinkin Duniya ya dakatar da ayyukansa tare da sallamar ma'aikatansa a yankin arewacin Yemen da ke hannun yan tawaye sakamakon tarnaki da cin zarafi da yan tawayen Houthi ke yi wa jami'an hukumar.
Shirin samar da abincin ya fara ne da jingine ayyukansa a watan Augusta a yankin yan Houthin da ke fama da rikici fiye da shekaru goma da suka wuce.
Akwai yiwuwar matakin zai kara ta'azzara halin tagaiyarar al'umma a kasar ta Larabawa da ke fama da yakin basasa tun 2014.
A cewar jami'an Majalisar Dinkin Duniya, dakatar da ayyukan zai shafi ma'aikata 365 na shirin abincin na MDD da suka rage a arewacin Yemen wadanda za su rasa aikin su daga nan zuwa karshen watan Maris.