Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi bayani kan cutar Hantavirus
May 8, 2026
Talla
Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce hadarin kamuwa da cutar hantavirus ga jama'a kadan ne bayan barkewar ta a wani jirgin ruwa.
Mutane uku ne dai suka mutu a jirgin MV Hondius, yayin da wasu kuma ake zargin sun kamu da cutar, lamarin da ya jawo damuwa a fadin duniya.
Hukumar ta lafiya a duniya WHO ta ce cutar ba wani sabon nau'in corona ba ce, kuma tana yaduwa ne ne kawai ta kusanci sosai, don haka hadarin ga sauran jama'a ya yi kasa.
Jirgin na kan hanyarsa zuwa tsibirin Tenerife da ke a kasar Spain, inda aka ce za a kwashe fasinjoji fiye da 140 domin tura su kasashensu.