1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Labarin Wasanni: Yadda ta kaya a karshen mako

Suleiman Babayo LMJ
May 4, 2026

Kungiyar da ke can kasar tebur wato Heidenheim, ta yi kokari wajen yin canjaras uku da uku da Bayern Munich da ke saman tebur da ma ta lashe kakar ta bana.

https://p.dw.com/p/5DFaH
Bayern Munich | Heidenheim | Bundesliga
Karan batta tsakanin Bayern Munich da HeidenheimHoto: Michelle Luka/STEINSIEK.CH/IMAGO

Haka ma dai abin yake tsakanin FC Union Berlin da FC Köln biyu da biyu. Ita kuwa Augsburg ta bi Werder Bremen har gida, ta kuma lallasa ta da ci uku da daya. Ita ma Hamburg ta bi Frankfurt har gida ta caskarata da ci biyu da daya. Haka kuma, an tashi wasa St. Pauli 1 Mainz 2 kana Monchengladbach 1 Dortmund 0 yayin da Freiburg da Wolfsburg suka tashi kunnen doki daya da daya.

La Liga | Real Madrid | Espanyol
Espanyol 0, Real Madrid 2Hoto: Lennart Preiss/AP Photo/picture alliance

Sai kuma yadda ta kaya a La liga ta Spaniya, inda a karshen mako aka fafata wasannin kamar haka:

Espanyol 0, Real Madrid 2

Villarreal 5, Levante 1

Valencia 0, Atletico 2

Alaves 2, Athletic Bilbao 4

Osasuna 1, Barcelona 2

Celta Vigo 3, Elche 1

Getafe 0, Rayo Vallecano 2

Betis 3, Oviedo 0

Premier League | Arsenal FC | Fulham
Arsenal 3, Fulham 0Hoto: Marvin Ibo Güngör/GES/picture alliance

A Premier League ta Ingila kuwa, an tashi wasannin a karshen mako kamar haka:

Arsenal 3, Fulham 0

Brentford 3, West Ham 0

Newcastle 3, Brighton 1

Wolverhampton 1, Sunderland 1

Bournemouth 3, Crystal Palace 0

Man United 3, Liverpool 2

Aston Villa 1, Tottenham 2

Serie A | Inter Mail | Kofi
Inter Milan ta lashe kofin Serie A na banaHoto: Spada/LaPresse/IMAGO

Kungiyar kwallon kafa ta Inter Milan, ta lashe gasar Serie A ta kasar Italiya ta bana kana karo na 21 a tarihinta. Kungiyar kwallon kafa ta Juventus na kan gaba wajen lashe gasar wasannin kwallon kafar na Italiya, inda take da kofuna 36. Inter Milan na biye mata a matsayi na biyu da kofuna 21, sai AC Milan a matsayin na uku da kofuna 19.

Ajantina | Diego Maradona
Marigayi Diego MaradonaHoto: Valterci Santos/action Plus/dpa/picture alliance

Hukumomin kasar Ajantina sun tuhumi kwararren likita kan halayyar dan Adam da hannu wajen mutuwar shahararren dan wasan kasar Marigayi . Shi dai likitan Carlos Diaz mai shekaru 34 a duniya, ya shaida wa kotun cewa tsohon dan wasan Maradona yana da matsalar sauya ra'ayi kuma ana bukatar ya daina shan barasa gaba daya kafin a iya yi masa magani. Kafofin yada labaran kasar ta Ajantina sun ruwaito cewa ana zargin likitan da sakaci wajen bayar da maganin da ya saba da cutar da ke damun Marigayi Maradona wanda ya yi fice a fagen kwallon kafa a duniya, abin da kuma ya yi sanadiyar mutuwarsa.

Tennis | Jannik Sinner | Nasara
Jannik SinnerHoto: Ana Beltran/REUTERS

Shahararren dan wasan Tennis na duniya wanda yake matsayi na farko a duniya cikin gwanayen wasan, ya lashe gasar da aka kammala a birnin Madrid na Spaniya. Ya zama dan wasa na farko, wanda ya lashe gasar sau biyar a jere. Shi dai Sinner lokacin wasan karshen, ya doke Alexander Zverev da 6-1 da kuma 6-2 cikin mintoci 57.

Linkaya | Gretchen Walsh
Gretchen WalshHoto: David Balogh/Getty Images

Ita ma 'yar wasan linkaya ta Amurka ta kafa sabon tarihin tseren yin linkaya ta baya na tsawon mita 100 da ta kammala cikin dakiko 54 da dan motsi, a yayin linkayar ta karshen mako. 'Yar wasan ta Amurka, ta dade tana kafa tarihi a fargen tseren linkaya a duniya a bangaren mata.

Rubutawa: Suleiman Babayo
Gyarawa da wallafawa: Lateefa Mustapha Ja'afar