1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
Ci raniAfirka ta Kudu

Korarrun 'yan Najeriya sun iso Legas daga Afirka ta Kudu

Michael Oti RM/ZMA
June 11, 2026

An fara jigilar 'yan Najeriya daga Afirka ta Kudu sakamakon rikicin korar baki da kuma rashin iznin zama a kasar.

https://p.dw.com/p/5FECx
Nigeria Lagos 2026 | Mann reagiert emotional nach Rückkehr aus Südafrika
Hoto: Sodiq Adelakun/REUTERS

 Shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa ya  fitar da tsare -tsare da zai magance mastalar shigowar bakin haure, yayin da matakin bai gamsar da masu suka ba.Tambayar da ake yi ita ce, shin wannan mataki zai magance mastalar korar baki da karfi da yaji?

Fifi dan shekaru 21 da ke buga kwallon kafa a club din Bucks Buccaneer da ke Premier Leagu din kasar Namibiya ya ce, ya je yawon shakatawa ne Afirka ta Kudu bayan da kakar wasa ta bana ta kare. Zanga -zangar kyamar bakin, ta rusta da shi. Fifi  wanda yana daya daga cikin wadanda aka kwashe zuwa Ghana ya ce, yana da niyyar buga kwallon kafa a club din kasar Afirka ta Kudu saboda kyan filayensu na  wasanni kamar yadda ya shaidawa DW:

"Sunana Fiifi ni dan kwallo ne daga Ghana shekarata 21, ina sha'awar kwallon kafa hakan tasa na nemi damarmaki a kasashen kudancin Afirka kamar Lesotho da Namibiya da South Afrka da kuma Swaziland. Bayan kakar wasan Namibiya da kulub din Backs Buccaneers, nazo hutu Afirka ta Kudu sai rikicin kyamar baki ya rutsa da ni. Na shiga kasar  bisa ka'ida, saboda hutu nazo. Babban abin da yasa dan kwalon kafa matashi kamar ni zai so zuwa Afirka ta Kudu shi ne, suna da filayen wasanni masu kyau da yadda suke daukar nauyin 'yan wansa da yadda tsarin lig dinsu yake. Gaskiya lig dinsu ya fi na Ghana."

Nigeria Lagos 2026 | Nigerianische Staatsbürger nach Flucht vor Xenophobie in Südafrika gelandet
Hoto: Sodiq Adelakun/REUTERS

Wannan muradin nasa, ya nuna yadda 'yan kasashen Afirka da dama suke da burin zuwa Afirka ta Kudu. Yankin kudancin Afirka musamman Afirka ta Kudu, ya kasance wurin da masu kaura daga nahiyar Afirkan ke muradin zuwa. Yankin kudancin Afirka da Afirka ta Kudu wurare ne dabam-dabam, sai dai masu kaura sun fi muradin shiga kasar ta Afirka ta Kudu saboda  damarmamaki na tattalin arziki da kuma kwanciyar hankali na siyasa a kasar. Hakan kuma ya sa kasar ta fi kowace kasa a Afirka, yawan bakin haure daga nahiyar.

Kiyasin Hukumar Kididdiga ta Afirka ta Kudu ya nunar da cewa, akwai bakin haure miliyan uku da 300,000 kusan sama da kaso biyar cikin 100 na yawan al'ummar kasar da ke da yawan mutane miliyan 65.Fredson Guilengue manajan shirye- shirye na Rosa Luxemburg Foundation a Johannesburg ya ce:

"Da ace nine shugaban Afirka ta Kudu, zan mayar da hankali ne kan samar da aikin yi. Afirka na bukatar aikin yi ne, kuma  cikin sauri wanda zai dauki matasa. Rashin aikin yi ga matasa ya yi kamari, abin da ke haifar da rashin zaman lafiya a zamantakewa. A dangane da haka, ya kamata Afirka ta Kudu ta zuba jari a wanan bangaren."

Nigeria Lagos 2026 | Repatriierte Nigerianer warten auf Registrierung am Flughafen
Hoto: Sodiq Adelakun/REUTERS

Yayin da yake bayani kan magance rikicin, Shugaba Cyril Ramaphosa ya bayyana jerin matakan da suke dauka don dakile shigowar bakin haure cikin kasar. Ya ce gwamnati za ta hukunta masu  karya dokar kaura ta kasar, wanda ya hada da tsaurara dokokinta na kan iyaka da kuma tsamo bata-gari a cikin  jami'an shige da fice. Sanann za ta hada kai da sauran kasashen Afirka don magance matsalar. Har ila yau,ya yi gargadi kan masu tare mutane da sunan neman takardun izinin zama a kasar.

Sai dai tabbacin da Shuga Ramaphosa ya bayar bai gamsar da masu zanga -zangar ba, domin kuwa kungiyoyi masu yaki da shigowar bakin haure kamar March and March sun ce maganar shugaban kasar mai ne kawai bisa ruwa.

Yayin da Ramaphosa yake tabbatarwa kasashen Afirka kokarinsa na magance matsalar, wa'adin ranar 30 ga watan yuni  da kungiyoyi masu yaki da bakin haure suka bayar na gab da cika. Kasashen Afirka da dama sun fara kwashe 'yan kasarsu, inda Ghana ke niyyar maka Afirka ta Kudu kotu a wani mataki na neman biyan diyya ga 'yan kasarta bayan hare-haren kyamar baki da aka kai musu.