1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
WasanniAsiya

'Yan sanda sun yi artabu da masoyan Messi a Indiya

Abdul-raheem Hassan
December 13, 2025

Masoyan Lionel Messi sun rusa shingen jami'an tsaro a wani filin wasa don yin tozali da gwaninsu yayin kaddamar da mutum-mutinsa mai tsawon kafa 70 da aka gina don karamashi a birn Kakola a gabashin kasar.

https://p.dw.com/p/55ICI
Dan wasan kwallon kafa Lionel Messi na ziyara a Indiya
Dan wasan kwallon kafa Lionel Messi na ziyara a IndiyaHoto: Dibyangshu Sarkar/AFP

Daruruwan masoyan dan wasan sun sanya da rigarsa tare da rera wakar girmama shi, wasu kuma sun fusata sun fasa alluna da kayan adon da aka tsara a filin saboda jami'an tsaro sun hana su shiga farfajiyar dukd a cewa sun sayi tikiti da kudi mai tsada da iyalansu don su yi ido hudu da tauraron dan wasan.

"A gare ni, kallon Messi abin farin ciki ne, mafarki ne. Amma na rasa damar da zan iya tabbatard a mafarkin saboda rashin tsarin gudanarwa mai kyau." a cewar wani dan kasuwa Nabin Chatterjee, mai shekaru 37.

Indien Kalkutta 2025 | Fans klettern nach Messis Abreise auf Torpfosten
Yadda wasu masoyan dan wasan suka makale a sama don ganin shiHoto: Sahiba Chawdhary/REUTERS

Wasu da dama sun sayi tikitin sama da dala 100 don wannan rana. "Na biya Rs 5,000 kwatankwacin da 55 na tikitin kuma na zo da dana don kallon Messi, ba 'yan siyasa ba, 'yan sanda da sojoji suna daukar hotun selfie, kuma masu gudanarwa ne ke da alhakin," Ajay Shah wani masoyin Messi.

An ga yadda 'yan siyasa suka yi ta rige-rigen daukar hotuna da dan wasan, yayin da dimbin masoyansa me ke nuna sha'awar daukar hotuna tare da shi. Dandalin ya rikide zuwa  tarzoma a lokacin da masoya suka fara jefin 'yan sanda da kwalabe, matakin da ya tilasta fitan dan wasan da wuri daga dandalin.

Yadda magoya bayan suka kakkarya kujeru da harbi a filin wasa
Yadda magoya bayan suka kakkarya kujeru da harbi a filin wasaHoto: Sahiba Chawdhary/REUTERS

Aved Shamim, wani babban jami'in ‘yan sanda a jihar, ya shaida wa manema labarai cewa, an kama babban mai shirya taron, ba tare da yin wani karin bayani ba. Linoel Messi mai shekaru 38, na rangadin kwanaki uku a Hyderabad da Mumbai da kuma New Delhi inda ake sa ran zai gana da Firaiministan Indiya Narendra Modi, a wani bangare na yawon ganawa da masoyansa a mastayin gwarzon dan wasan kwallon kafa na wannan zamani.

Messi ya lashe kyautar gwarzon dan wasan da ya fi kowa daraja a gasar Major League Soccer a karo na biyu a jere a wannan makon, bayan da ya akalar Inter Miamilashe gasar MLS kuma shi ya fi yawan kwallaye a gasar.

Tsohon dan wasan na Barcelona da Paris Saint-Germain, zai jagoranci kasarsa Argentina karekofin duniya da ke hannunta a gasar da za a fara a watan Yuni zuwa Juli a Arewacin Amurka.