'Yan tawaye sun bukaci sojojin Rasha su fice daga Mali
April 29, 2026
‘Yan tawayen Abzinawa sun bukaci dakarun Rasha su fice daga "dukkan ƙasar Mali.”
Kakakin ƙungiyar haɗin gwiwa ta Abzinawan Mohamed Elmaouloud ne ya shaida wa AFP wannan bukatar a ranar Laraba.
Assimi Goita ya ce an yi nasarar dakile 'yan ta'adda a Mali
A ƙarshen mako, ‘yan tawayen tare da hadin gwiwar wasu kungiyoyin 'yan ta'adda sun kai hare-hare kan muhimman wuraren gwamnatin soja, ciki har da yankunan da ke kusa da babban birnin ƙasar, Bamako.
Maharan sun ƙwace garin Kidal da ke arewacin ƙasar yayin da Ministan Tsaro, Janar Sadio Camara, wanda ake kallonsa a matsayin jagoran sauya akalar gwamnatin sojan Mali zuwa Rasha, ya mutu bayan kwanaki biyu na fafatawa mai zafi da 'yan ta'adda.
Shugaban gwamnatin Mali ya bada tabbacin tsaro bayan harin 'yan ta'adda
Ya kuma bayyana cewa ‘yan tawayen na kallon shigar Rasha cikin rikicin a matsayin babban laifi.