SiyasaGabas ta Tsakiya
'Yan tawayen Houthi na Yemen sun harbo jirgin yakin Amurka
September 16, 2024
Talla
'Yan tawayen Houthi na Yemen sun yi ikirarin kakkabo wani jirgin Amurka marar matuki a Litinin din nan, inda wani faifan bidiyo ya nuna yadda suka harba makami mai linzami har ya harbo jirgin, sannan hayaki ya turnuke bayan tarwatsewarsa a yankin Dhamar.
Karin bayani:Amurka ta kai hari kan tungar 'yan tawayen Houthi na Yemen
To sai dai Amurkan ba ta ce komai ba game da wannan ikirari na Houthi.
Karin bayani:Amurka ta kai sabbin hare-hare kan Houthi a Yemen
Mai magana da yawun kungiyar Birgediya Janar Yahya Saree, ya ce sunan jirgin da suka harbo MQ-9 Reaper drone, kirar Amurka.