Yau ake cika shekaru hudu da yakin Ukraine
February 24, 2026
Shugabar Hukumar Gudanarwar Tarayyar Turai Ursula von der Leyen da Shugaban Zauren Majalisar EU António Costa na daga cikin mayan bakin da ke ziyara a birnin Kiev, don sake jaddada goyon baya ga Ukraine. Shugabannin na EU za su ziyarci tashar makamashin Ukraine da dakarun Rasha suka kai wa farmaki a kwanakin da suka gabata.
Karin bayani:Shugaban Ukraine ya ce Rasha ta fara yakin duniya na uku
Haka zalika, shugabannin kasashe mambobin EU da ke goyon bayan Moscow, wato Hungary da Slovakia za su halarci taron. Shugaban Faransa Emmanuel Macron da Firaministan Burtaniya Keir Starmer za su shiga taron amma ta intanet tare kuma da jaddada mubayi'a ga gwamnatin Kiev.
Karin bayani:Ana dab da cika shekaru hudu da farmakin Rasha a Ukraine
A can kuwa birnin Berlin, Shugaban kasar Jamus Frank-Walter Steinmeier da Ministan Harkokin Waje Johann Wadephul , za su gudanar da wani 'dan kwarya-kwaryar taro na nuna alhini da kuma goyon baya ga Ukraine. Baya ga birnin Berlin ana sa ran gudanar da gangamin goyon bayan Ukraine din a biranen Jamus da suka hada da Bremen da Stuttgart da Munich da kuma birnin Cologne.