1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yaushe za a ga 3 Khans a fim daya?

Abdul-raheem Hassan Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
November 30, 2025

Sama da shekaru 30, fitattun jaruman na Bollywood "Khans" na jan zarensu ba tare da an dena yayinsu ba a sinimun kasar Indiya. Tun a karshen 1980s da jaruman suka fara tashe, haryanzu ba su taba fitowa a fim daya ba.

https://p.dw.com/p/52QnL
Jaruman Bollywood Salman Khan da Shah Rukh Khan da Aamir Khan
Jaruman Bollywood Salman Khan da Shah Rukh Khan da Aamir Khan

Me ya sa ba a taba ganin taurarin Bollywood din nan guda uku a fim daya ba? Rashin mai kudin da zai iya biyansu duka a lokaci da, iko ko dai babu kwararren daraktan da zai iya sarrafa jaruman a fim daya - wadannan kadan daga irin tambayoyin da ke saka a zukatan yawancin masu bibiyar fina-finan Indiya sama da shekaru 30 kenan, kodayake, an ce ba a sarakai uku a fada daya wannan ya sa muka nazarci batun don samar da amsa.

Fuskokin jaruman guda uku sun mamaye idanun masu kallon fina-finai a ko wane lungu da sako na duniya. Jaruman sun yi fice a fannoni daban-daban da har ta kai su ga lashe lambobin yabo a ciki da wajen kasar Indiya, inda suka tara dukiya mai tarin yawa da kuma dimbin masoya a duniya. To amma rashin ganinsu tare a cikin fim daya, ya sanya ayar tambaya tare da janyo muhawara iri-iri.

Shah Rukh Khan's Film 'My Name Is Khan'
Fostar fim din Shah Rukh Khan mai suna 'My Name is Khan' Hoto: picture alliance/dpa

Yaushe jaruman suka fara? A karshen 1980s da farkon 1990s, Khans sun fara tashe a kusan lokaci guda, amma kowa hanyarsa daban.

Indien Mumbai 2025 | Aamir Khan kündigt YouTube-Veröffentlichung von 'Sitaare Zameen Par' an
Jarumi Aamis Khan, a taron manema labarai a MumbaiHoto: Indranil Aditya/ZUMA Press Wire/IMAGO

Aamir Khan: 'Mr. Perfectionist' wato gwani na gwanaye, an haifi jarumin a watan Maris na shekarar 1965, ya zama "Jarumi mai kaifin tunani" ya fara nuna kaifin basirarsa a fina-finai kamar Qayamat Se Qayamat Tak da aka shirya a shekarar 1988 da Lagaan wana aka yi  a 2001, an gina fina-finan a kan kamala da kuma ingantaccen labari. Fim din Lagaan da 3 Idiot da PK da Dangal da kuma Taare Zameen Par na cikin fina-finai kusan 50 da jarumin ya shirya, wanda ya ba shi yawan mabiya kusan miliyan 25 a shafukan sada zumunta. An kiyasta jarumin ya mallaki arzikin da ya kai akalla dala miliyan 250. Mahaifinsa fitaccen marubuci ne jarumi kuma mai ba da umarni, wato Tahir Hussain, haka zalika kanin mahaifinsa wato Nasir Hussain. 

Salman Khan: Jarumi dan 'kwalisa', wanda dan gado ne, domin ko mahaifinsa Salim Khan fitaccen marubucin fina-finai ne, yana da yawan mabiya sama da miliyan 65 a Instagram kadai, ya fara sace zuciyar masu kallo da tsantsar fara'arsa da kamalarsa, inda ya zama zakaran gwajen dafi a fina-finan fada da na soyayya. Misali fim din Maine Pyar kiya wana aka yi a shekarar 1989 da kuma Dabangg na shekarar 2010 kuma ya fito a fina-finai sama da 100.

Jarumi Salman Khan, yayin daukar fim dinsa mai suna Tiger a shekarar 2017
Jarumi Salman Khan, yayin daukar fim dinsa mai suna Tiger a shekarar 2017Hoto: Everett Collection/picture alliance

An haifi jarumin a watan Disamban shekarar 1965, an kiyasata arzikinsa kusan sama da dala miliyan 80. Jarumin yana cikin jaruman fina-finai da rayuwarsu ke fuskantar barazana. Tsawon shekaru jarumin ke tsallake rijiya da baya sakamakon yadda aka sha kai masa hari da bindiga domin halaka shi, a dalilin harbe wata dabba da ya yi a lokacin farauta, wadda ke zama abar bautar wasu mutane. Ya yi farautar a yayin daukar fim din Hum Saath-Saath Hain a shekarar 1998. Jarumin yana da gidauniya ta musamman da ke taimakawa marayu da gajiyayyau a cikin Indiya, jarumin ce zai samu yaro nan ba da jimawa ba duk da cewa bai yi aure ba.

Shah Rukh Khan: Kamar yadda wasu ke masa lakabi da "Sarkin soyayya", an haife shi a shekarar 1965 a birnin New Delhi. Ya fara baje kolin baiwarsa tun a fina-finan Dilwale Dulhania Le Jayenge da aka shirya 1995 da Kuch Kuch Hota Hai da ya mamaye zukatan 'yan kallo a shekara 1998. Khan ya yi fina-finai sama da 80 wadanda suka ya sanya shi zama fuskar Bollywood a duniya, inda ake masa lakani da King Khan.

Jaruma Deepika Padukone da Shah Rukh Khan a cikin fim din Pathaan
Jaruma Deepika Padukone da Shah Rukh Khan a cikin fim din PathaanHoto: DESI ENTERTAINMENT PARIS

Ya zama jarumin Bollywood na farko da ya mallaki arzikin da ya kai sama da dala biliyan daya. Sai dai dansa mai suna Aryan bai bi sahun mahaifinsa ba a fannin fitowa a fim, inda ya zabi zama mai ba da umarni wato Director. 

Kamar yadda ko wannensu ya gina ta sa daula, haka ma fina-finansu suka fara banbanta, ko wane Khan dai ya zama jigon duniyarsa.

Me ya ke hana taurarin haduwa a fim daya?

Daukaka da jin kai: A Bollywood, taka babban matsayi a fim gagarumin kasuwanci ne mai matukar muhimmanci, lamarin da nuna cewa akwai tarin tambayoyi masu sarkakiya kan ko waye kan gaba a ciki wadannan manyan taurari uku a masaana'antar, shin wanene ya fi daukar hankali ?

Karin bayani: Masu shirya fina-finan wato producers a turance, da masu ba da umarni, sun dade da sanin cewa hada jarumai irin wadannan a lokaci guda zai fuskanci babban kalubale. Shah Rukh Khan ya taba furta wata kalma cikin raha a shirin tattaunawa da jarumai na fitaccen mai shirya fina-finai Karan Johar, wato Koffee With Karan: inda ya ce "Idan kun sanya duka uku a cikin fim ɗaya, zai zama babban al'amari ga masu shiryawar. Wanene zai sami fifiko ? Ku manta da masu sauraro - za mu yi gumurzu a tsakaninmu !"
Duk da cewa ya fadi hakan cikin raha, akwai kamshin gaskiya a zancensa. Ko wane Khan yana son iko a kan ayyukansa. Don haka, a sani cewa duk aikin da zai hada jaruman, dole a daidaita muradin kowa, kama daga jiji da kai da nuna iyawa, wanda kuma ba kasafai ake samun irin haka ba a Bollywood.

Bambancin falsafa da tsarin fina-finai: Banbance-banbance da ke tsakanin jaruman guda uku da ake yi wa lakabi da Khans bai tsaya ga ra'ayi ba, har ma a fannin fasaha sun banbanta. Aamir Khan yana bin tsarin kirkira da zahiri yayin da Salman Khan ya fi mayar da hankali a kan nishadantarwa da magoya baya ke yi. Shah Rukh Khan ya karkata ne kan tsarin jan hankalin masu kallo cikin salo mai taba zuciya. 

Salon fina-finansu ba kasafai suke tafiya tare ba, dalilin kenan da ya sanya za a sha gwagwarmayar rubuta labarin da zai bai wa kowa damar taka rawa yadda yake so a fim guda.
Salman Khan ya taba cewa: "Mutane suna so su ga dukkanmu uku tare a cikin fim daya, amma me za mu yi? Muna da buri daban-daban. Watakila idan aka samu babban labari na musamman mai ban sha'awa, za mu yi tunanin hakan."

Salman Khan da Shah Rukh Khan a bikin auren Anant Ambani
Salman Khan da Shah Rukh Khan a bikin auren Anant AmbaniHoto: Reliance/AP Photo/picture alliance

Me ya tarwatsa shirin hada jaruman uku a fim daya a baya?

Aamir da Salman sun fito a fim daya mai suna Andaz Apna Apna a shekarar 1994, wanda na barkwanci ne da a farko bai karbu ba, sai daga baya ya birge masu kallo, har aka ci kasuwarsa sosai.
Haka zalika Shah Rukh da Salman sun fito tare a fim din Karan Arjun a shekarar 1995, wanda ya zamto gagara gasa sakamakon karbuwa da ya samu a duniya, har ya shiga jerin fina-finai masu tarihi sosai a shekarun.
Jaruman sun yi fitowa ta musamman a wasu fina-finansu, a wani mataki na karfafa alaka da abota. Alal misali, Salman ya fito a fim din SRK mai suna "Zero”, shi ma Shah Rukh ya fito a fim din Salman mai suna "Tubelight”.

Kamar yadda Aamir ya taba fada cikin raha: "Ina tsammanin ranar da muka yi fim tare, box office zai tumbatsa - ko kuma gidan kallo ya rushe!"

Ko akwai sauran fata na ganin 3 Khans a fim daya? 
Kusan kowace shekara, ana sabunta jita-jitar hada manyan jaruman a fim daya. Daraktoci kamar Rajkumar Hirani da Karan Johar da kuma Farah Khan sun nuna sha'awar tabbatar da wannan mafarki, sai dai ana tsamun tseko yayin tsarawa da rubuta labari.

Ganin yadda fitattun jaruman uku ke zabar matsayi da man'yan fina-finai, fatan ganin jaruman a fim daya na disashewa. Kodayake, Bollywood ta sama sammatar mutane da abin mamaki, don haka masu kallo ba su yanke kauna ba.
Shah Rukh Khan ya taba cewa: "Idan an samu labarin da ya yi daidai, kuma lokacin ya yi, za mu yi shi. Amma kafin lokacin, mu cigaba da jin dadin fina-finan juna."

Rashin samun gagrumin fim daya da ya hada manyan taurarin Bollywood din guda uku wato "Khans" ba gazawa ba ne - alama ce da ke nuna yadda zamani ke sauya salo duniyar Bollywood. Ko a gansu tare ko akasin haka, Aamir da Salman da kuma Shah Rukh Khan sun ci gaba da murza kambunsi a sinimun kasar Indiya, sun kuma kafa tarihin rike kambunsu na tsawon lokaci fiye kowane jarumi a masana'antar.

Ana alhinin mutuwar Dhramendra