1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zamfara: Zanga-zangar mata kan tabarbarewar tsaro

April 29, 2026

Matan daga garuruwa 15 da 'yan bindiga suka kora sun toshe hanya ba shiga ba fita saboda abun da suka ce, cigaba da halaka mutane amma har yanzu babu abunda mahukuntan ke yi

https://p.dw.com/p/5D0X7
Nigeria Freilassung der enführten Schülerinnen
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

Al'umma sun ce koka da janye jami'an tsaro da ke basu kariya shi ya sa 'an bindigar ke ci gaba da kai masu hari babu kakkautawa.  Masu zanga-zangar daga garin Lilo da wasu garuruwan mafi akasari mata da kananan yara dauke da kaya, inda suka tare hanyar Kwatarkwashi da ta hada jihohin Sokoto da Kebbi da kuma Katsina abunda ya sa motoci suka yi dafifi ba wucewa.

"Fati ni ke, dalilin zanga-zanga wahalar duniya ta ishemu. Kullun muna cikin fargaba, har an bamu jami'an tsaro, yanzu sun je sun dauke abunsu .Yanzu a karshe ma suna can sun likama garin wuta kuma duk abunda suka yi niyyar yi sun yi suna can suna cigaba da ta'asar su".

Gouverneur des Bundesstaates Zamfara, Dauda Lawal Dare
Hoto: Dauda Lawal/Facebook

Al'ummar Garuruwan kananan hukumomi uku ne suka hadu suka tare hanyar kuma fatansu mahukunta su magance masu damuwarsu, saboda idan ba sun fito titi ba to ba za'a gane halin da suke ciki ba saboda inda suna lungu tamkar ihunka banza ne kamar yadda wannan hakin yankin ke cewa;

"Sunana Murtala Sabon Gari hakimi a garin Lilo, a gaskiya garuruwan sun kai 15 hade muke maza da mata. To yanzu kasancewar abubuwa sun yi nauyi shi ne dalilin da ya sa muka fito domin neman mafita wurin mahukunta da kuma Allah. Gaskiya har yanzu babu wani agaji da muka samu".

Gwamnatin Jihar Zamfara ta tabbaar da wannan zanga-zanga amma dai ta ce tana shawo kan lamarin a cewar mai bai wa gwamnan jihar ta Zamfara shawara kan harkokin tsaro Ahmed Danmanga.

Nigeria JSS Sicherheitskräfte in Jangebe
Hoto: Afolabi Sotunde/REUTERS

"Gwamnati ba ta san abun da ya faru ba sai daga baya bayan fitowarsu. Gwamnati ta san akwai jami'an soja a garin Lilo wadanda aka kai su zauna wurin amma ba'a san da fitowarsu ba, saboda gwamnati ba za ta bari akwai talakawa a gari ba ace a janye jami'an tsaro to ta wane dalilin? To amma an tura jami'an mofal na 'yan sanda da gaggawa don su gaggauta zuwa garuruwan nasu ga halin da ake ciki, bada sanya ba sun yi kokarin zuwa inda suka tarar mutanen har sun fara kone-kone amma jin ga jami'an tsaro nan sun zo sai suka gudu suka koma maboyar su".

Kamarin hare-haren 'yan bindigar na zuwa ne lokacin da damina ke karatowa a arewacin Nigeria shin ko mahukunta zasu samarwa al'ummar tsaro su samu isasshiyar damar yin noma a daminar bana.