1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Shekaru 15 bayan fara zanga-zangar Libiya

Mouhamadou Awal Balarabe ZMA
February 16, 2026

Cikin yanayi na kwarya-kwaryar kwanciyar hankali a Libiya, Majalisar Dinkin Duniya ta sake kaddamar da shawarar shirya zabe.

https://p.dw.com/p/58qs2
Muammar al-GaddafiHoto: Abdel Magid Al Fergany/AP Photo/picture alliance

Shekaru 15 da suka gabata ne ake gudanar da zanga-zanga a Benghazi, birni na biyu mafi girma a kasar Libiya don neman a saki wani mai fafutuka. Sai dai sakamakon matsin lamba da musgunawa, boren ya rikide zuwa juyin juya hali da a karsheya kawo karshen gwamnatin Muammar Gaddafi. Tun daga wannan lokaci ne Benghazi ke fuskantar rudani.

Akram Hamad Amsallem, yana tune da abubuwan da suka wakana daga 15 zuwa 20 na watan Fabrairun 2011 a bakin tekun Benghazi. A Lokacin da aka fara zanga-zangar neman sakin mai fafutuka, wannan dan sandan ya ki bin umarnin hukumomi inda shi da abokan aikinsa suka ki harbin masu zanga-zangar.

"An haife ni a wannan birni. Na yi karatu a nan, kuma ina zaune a garin. Kuma abin da ya sa na bi mutane shi ne, ina son in ba da gudunmawa wajen gina wannan birni. Ko a cikin rundunar 'yan sanda a zamanin gwamnatin Gaddafi, akwai cin hanci da rashawa."

Masu zanga-zangar adawa da Gaddafi
Masu zanga-zangar adawa da GaddafiHoto: picture-alliance/dpa/M. Messara

Rayuwa a Benghazi shekaru 15 bayan Gaddafi

Shekaru 15 bayan zanga-zangar da ta rikide zuwa hambarar da Moammar Gaddafi, rayuwa ta canza sosai a birni na biyu mafi girma a Libiya. Hasali ma dai, Akram Hamad ya rasa kafarsa daya a watan Afrilun 2014, sakamakon hare-haren da masu tsattsauran ra'ayi ke kaiwa kan jami'an tsaro da alkalai.

Amma dai wata guda bayan haka, Khalifa Haftar ya fara sa kafar wando guda da 'yan ta'adda da ke tsoratar da mazauna birnin Benghazi. Alal hakika ma dai, birnin da ke zama tushen juyin juya halin ya jure ma shekaru uku na yaki mai tsanani da ya lalata ababen more rayuwa. A yanzu haka ma dai, birnin ya fara murmurewa sannu a hankali. Amma Akram Hamad, ba ya nadamar abin da ya faru.

"Mun dandana kudarmu, har da ni kaina. Janar Khalifa Haftar ya taka rawa mai cike da tarihi ta hanyar ayyana yaki a cikin mawuyacin hali da karancin albarkatun yaki da karancin soja. Ina matukar farin ciki da abin da nake gani a yau, kamar wadannan yara da ke wasa."

Rikicin madafan iko na gwamnatocin Libiya

Sai dai wannan ci gaba ya zama na mai hakon rijiya a Libiya saboda har yanzu kasar na cikin mawuyacin hali. Tun daga shekarar 2014, gwamnatoci biyu na fafatawa da juna don neman kakkange madafun ikon Libiya. Yakin karshe ya samo asali ne a shekarar 2019 lokacin da Khalifa Haftar, wanda ke iko da Gabas da kudancin LibIya ya yi yunkurin kai hari kan babban birnin Tripoli a Yamma. Sai dai shekara guda bayan haka, sojojinsa sun ja da baya.

Khalifa Haftar
Khalifa Haftar Hoto: Abdullah Doma/AFP/Getty Images

Ahmed Ben Achour, yana da zama yanzu haka a Benghazi. Amma da kamar wuya wannan mai gabatar da shirye-shiryen talabijin, wanda ya goyi bayan Khalifa Haftar, ya koma garinsu Tripoli. Amma duk da haka yana da kyakkyawan fata game da makomar Libiya.

"Tun daga shekarar 2020, 'yan Libiya sun san cewa yaki ba mafita ba ne. Ko da akwai rikici yanzu haka, amma ya shafi siyasa ne da tattalin arziki. Babu alaka da batun makamai a yanzu."

Yunkurin shirya sabon zaben kasa baki daya

A wannan yanayi na kwarya-kwaryar kwanciyar hankali a Libiya, Majalisar Dinkin Duniya ta sake kaddamar da shawarar shirya zabe, kamar yadda Stéphanie Koury, mataimakiyar shugaban ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Libiya ta bayyana.

"An dade ana jiran zaben kasa. An gudanar da zaben karshe a shekarar 2014. Kuma shi ya sa muke bukatar zabe: yana ba da tabbacin dora alhakin masu zabe a kan jami'ai da aka zaba. Duk wadannan matakai suna da mahimmanci wajen karfafa ma'aikatu da cibiyoyin kasar Libya.

A shekarar 2021 ma an sanar da shirya zabe a Libiya, amma har yanzu shuru kake ji tamkar an shuka dusa.