1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Zanga-zanga ta barke a Spain

October 26, 2025

Zanga-zangar ta birnin Valencia na zuwa ne shekara guda bayan aukuwar mummunar iftila'in ambaliyar ruwa a Spain.

https://p.dw.com/p/52afb
Zanga-zanga ta barke a Spain shekara daya bayan mummunan ambaliyar ruwa
Zanga-zanga ta barke a Spain shekara daya bayan mummunan ambaliyar ruwa Hoto: Alex Juarez/Anadolu/picture alliance

Dubbun dubatar mutane ne a Spain sun gudanar da zanga-zangar a birnin Valencia da ke gabashin kasar, yayin da ake cika shekara guda da aukuwar mummunan ambaliyar ruwan da ta yi sanadin rayukan mutane 229. Masu boren na neman shugaban yankin, Carlos Mazon ya aje mukaminsa sakamakon yadda bai mayar da hankali ba a lokacin da iftila'in ya auku ba. Masu zanga-zangar rike da kwalaye sun yi ta tada jijiyoyin wuya suna cewa, dole ne a tesa keyar Mazon zuwa gidan kaso tare da zargin cewa, wadanda iftila'in ya ruutsa da su ba mututwa suka yi ba kashe aka yi.

Karin bayani: Wadanda suka rasu a ambaliyar Spain sun zarta 200

An dade ana zargin gwamnatin Mazon da rashin bayar da gargadi kan ambaliyar a kan lokaci. Al'ummar kasar sun ce har sai da ruwa ya fara bulbulowa daga kasa yana malala a kan hanyoyi zuwa cikin gidajen mutane kafin su fara samun gargadi. Sai dai Mazon ya ce gwamnatinsa na da karanci sahihan bayanai na bayar da gargadi da wuri.