1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Afirka ta Kudu ta kori baki dubu uku 'yan kasashen Afirka

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
June 14, 2026

Ghana da Najeriya da wasu kasashen Afirka sun fara kwashe mutanensu sakamakon zanga-zangar adawa da baki 'yan Afirka.

https://p.dw.com/p/5FO9o
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril Ramaphosa
Shugaban Afirka ta Kudu Cyril RamaphosaHoto: Willy Kurniawan/REUTERS

Afirka ta Kudu ta sanar da mayar da baki 'yan kasashen waje kimanin 2,745 zuwa kasashensu na asali a cikin mako guda, a kokarin da shugaban kasar Cyril Ramaphosa ke yi na yaki da kwararar bakin haure marasa izinin shiga kasar.

Karin bayani: Rikicin 'yan daba ya halaka mutane 12 a Afirka ta Kudu

Ministan harkokin cikin gida na kasar Leon Schreiber ne ya tabbatar da hakan ga manema labarai a wannan Lahadi.

Afirka ta Kudu na zama kasa mafi karfin tattalin arziki a nahiyar Afirka, to amma tana fama da matsalar rashin aikin yi, wanda ya kai matakin kashi 30 cikin 100.

Karin bayani: Dawo da 'yan Ghana daga Afirka ta Kudu ya dauki hankalin jaridun Jamus

A baya bayan ne Ghana da Najeriya da wasu kasashen Afirka suka fara kwashe mutanensu da ke zaune a kasar, sakamakon zafafar zanga-zangar adawa da baki 'yan kasashen Afirka.