Haiti: Bukatar kafa sabuwar runduna don murkushe 'yan daba
September 22, 2025
Amurka da Haiti sun yi kira da a sauya fasalin tawagar jami'an tsaro ta kasa da kasa da ke taimakawa 'yan sandan tsibirin Haiti zuwa wata runduna ta musamman da za ta murkushe kungiyoyin 'yan daba, gabannin kuri'ar da kwamitin sulhu na MDD zai kada nan ba da jimawa ba.
A makwannin da suka shige Amurka da Haiti sun kaddamar da tattaunawa a kwamitin sulhu na MDD domin canja rundunar MMAS da aka samar a 2023 kuma Kenya ke jagoranta zuwa rundunar murkushe 'yan daba da suka hana al'ummar Haiti sukuni.
Karin bayani: Rikicin 'yan daban Haiti ya halaka mutane 5,600 a 2024
Kasashen biyu sun kafa hujja da raunin rundunar wadda wa'adinta ke karewa a farkon watan Oktoba, sannan kuma a cewar shugaban rikon kwaryar Haiti rashin isassun kudaden gudanarwa da kayan aiki da kuma jami'ai ya sa har yanzu an gaza kawo karshen 'yan dabar da ke cin karensu babu babbaka.
Bayanai na nuna cewa sabuwar rundunar da za a samar bisa shawarar Amurka da Panama za ta kunshi jami'an tsaron kusan 6,000 da suka hada da 'yan sanda da kuma sojoji, sai dai shirin na iya gamuwa da turjiyar China da Rasha da ke kujerun dindindin a kwamitin sulhun na MDD.