1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Amurka ta kakkabo jirginta marar matuki bisa kuskure a Texas

Abdulkarim Muhammad Abdulkarim
February 27, 2026

Rahoton Reuters ya nuna cewa shelkwatar tsaro ta Pentagon ta harbo jirgin ta hanyar amfani da garkuwar sararin samaniya.

https://p.dw.com/p/59Udn
Yadda sojin Amurka na National Guard ke sintiri a yankin El Paso na jihar Texas mai iyaka da Mexico
Yadda sojin Amurka na National Guard ke sintiri a yankin El Paso na jihar Texas mai iyaka da MexicoHoto: Kaylee Greenlee Beal/REUTERS

Rundunar sojin Amurka ta kakkabo jirgi marar matuki mallakin gwamnati bisa kuskure, lokacin da yake shawagi a jihar Texas, mai iyaka da kasar Mexico, lamarin da ya tilasta hukumar kula da sufurin jiragen sama ta kasar dakatar da zirga-zirgar jirage a yankin.

Karin bayani - Sojin Mexico sun kashe gawurtacen mai safarar muggan kwayoyi

Wani kusa a gwamnatin Amurka ya tabbatarwa kamfanin dillancin labarai na Reuters yadda shelkwatar tsaro ta Pentagon ta yi amfani da garkuwar sararin samaniya, wajen harbo jirgin bisa kuskure.

'Yan majalisar dokokin Amurka na jam'iyyar adawa ta Democrats, Rick Larsen da Bennie Thompson da kuma Andre Carson, wadanda ke cikin kwamitocin kula sufurin jiragen sama da harkokin tsaron cikin gida, sun soki yadda lamarin ya faru, inda suka ce rashin hadin gwiwa tsakanin hukumomin kasar ne sanadiyyar wannan hadari.