1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAmurka

Tattaunawa domin warware rikicin Ukraine

Abdourahamane Hassane
November 25, 2025

An gudanar da tarurruka a asirce a kan Ukraine tsakanin Amurka da Rasha sannan za a ci gaba da tattaunawa a Abu Dhabi domin samun mafita a yakin da ake yi tsakanin Rasha da Ukraine.

https://p.dw.com/p/54D1n
Mun yin amfani da tsohon hoto
Mun yin amfani da tsohon hotoHoto: Fabrice Coffrini/AFP/Getty Images

Ana gudanar da taron ne domin cimma yarjejeniyar  tsagaita wuta, kamar yadda kafofin watsa labarai na Amurka da Birtaniya suka bayyana.

A cewar  kafofin, sakataren rundunar sojin Amurka  Dan Driscoll shi ne ke jagorantar tawagar Amurka. Yayin  da shugaban hukumar leken asirin sojojin na Ukraine ya wakilci kasarsa.

Sai dai ana  gudanar da wannan  tattaunawa ce yayin da  Ukraine da Rasha suka ba da rahoton kai  hare-hare ta sama.

 Inda aƙalla mutane uku suka mutu a yankin Rostov na Rasha da wasu  shida a ɓangaren Ukraine, inda aka sake kai hari kan ɓangaren makamashi da babban birnin Kyiv. Abu Dhabi.