Amurka ta kama jirgin dakon man fetur na Najeriya
December 12, 2025
Wani katon jirgin dakon danyan mai da ya tashi daga ruwan Tekun Najeriya ya nufi Amurka, ya fada hannun jami'an tsaron kasar ta Amurka, bisa zargin ya na dauke da danyan man sata. Kuma wani bincike da hukumomin na Amurka ke yi yanzu kan wannan jirgi, ana tunanin zai bankado wata karin madakalar safarar muggan kwayoyi, da kuma assasa harkokin barayin kan teku, da munin tasirin sake shafar kasashe da dama.
Ba tun yanzu ba ne ba dai ake ta magana kan katutun satar danyan mai da ke wakana a yankin da ke da arzikin mai a kasar wato Niger Delta.
Bayanan da ake da ciki
Bayanan kama wannan Katafaren jirgin dakon danyan mai, mai suna Super Tanker, wanda kuma ake zargin na makare da danyan man sata da ya shiga kasar Amurka ta ruwa daga Najeriya, na nan a tsare a hannun jami'an tsaron na Amurka, inda bayanai ke nuna cewar, an fara gudanar da wani binciken kwakwaf kansa, kan wata alaka da ake zargin jirgin na da ita da takidin safarar muggan kwayoyi da harkokin barayin kan teku, wadda ke da munin tasiri a musamman zirin tekun Gunea da ke addabar kasashe da dama, ciki har da Najeriya, da Kamaru da Sao Tome, Ghana da sauransu.
Jirgin na ruwa dai mai lamba 9304667 mallakin wani babban dan kasuwa a Najeriya da ke da kamfanin Thomarose Global Ventures, jami'an tsaron na Amurka, sun ankara ya yi ba-sajan makala tutar wata kasa ta daban maimakon ta Najeriya yayin dosowa ta Ruwan na Amurka, wadda hakan ya sa kokwanto kan jirgin da ma jami'an da ke tafiyar da jirgin, inda daga bisani kuma aka gano jirgin ba ya cikin tsarin jiragen da ake dako a hukumance.
Alkaluma da suka fita a watan jiya na Nuwamban shekarar 2025, sun nuna cewar Najeriya ta yi hassarar kimanin kudi Dala biliyan 300 kawo yanzu, sakamakon satar danyan man Najeriya, a ciki da wajen kasar.
Satar danyan man Najeriya dai da sau tari kan bar baya da kurar gurbata muhalli, na ci gaba da kassara yankin mai arzikin mai na Niger Delta.