1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Takun saka tsakanin Dangote da PENGASSAN

September 29, 2025

A yayin da rikici yake kara sama a tsakanin ma'aikata da matatar Dangote, kungiyar manyan ma'aikatan man fetur ta kasar PENGASSAN ta tsunduma wani yajin aikin da ya tsaida aiyyuka a kusan duk harkar mai na Najeriya.

https://p.dw.com/p/51EYH
Wani bangaren Kamfanin man Aliko Dangote
Kamfanin man Aliko DangoteHoto: Temilade Adelaja/REUTERS

 

Daukacin masana'antar man fetur a Najeriya ta tsaya cak, sakamakon wani yajin aiki na kungiyar PENGASSAN ta manyan ma'aikatan man fetur.

Duk da kokari na tsomin baki a bangaren mahukuntan Najeriya dai daga duk alamu an yi tsaiwa irin ta gwamen jaki a tsakanin 'yan kungiyar PENGASSAN da ke fadin matatar ba ta da ikon korar ma'aikata bisa 'yancinsu, da kuma Dangoten da ke fadin ta kare.

Yajin aiki ya kankama

Aliko Dangote attajiri dan Najeriya
Aliko Dangote attajiri dan NajeriyaHoto: Adam Abu-bashal/Anadolu Agency/picture alliance

Tun da sanyi na safiyar yau dai ne ma'aikata suka sa sarka suka rufe ofisoshi da hukumomi da ke kula da harakar man , a wani abun da ke kama da kokari na aike sako.

Koma ya zuwa ina yajin aikin ke shirin ya kai a kokari na gwajin kwanjin a tsakanin na kungiyar PENGASSAN da matatar Dangote, dai kokari na ji ta baki na matatar dai ya kare tare da kakaki na kamfanin Dangoten Tony Chiejina gaza mai da martini bisa tambayoyin da na aike masa.

Masu neman man fetur a Najeriya
Masu neman man fetur a NajeriyaHoto: DW

To sai dai kuma tun da farkon fari dai wata sanarwa ta kamfanin ta zargi kungiyar da kokari na ta'addanci. Dangoten da ya ce ya kori ma'aikatan bisa kokarin zagon kasa dai, ya ce kokarin kare kaddarorinsa ne ya kai shi ga sallamar da ta tada hankali.

Zargin babakere

An dade ana zargin Dangote da kokarin babakere cikin batun hajjar man fetur mai tasiri. Kuma kama daga ita kanta gwamnati ya zuwa ga kamfanin NNPC da hukumomin da ke kula da harkar man dai duk sun raba gari da Dangoten kafin sabon rikicin ma'aikatan .

Najeriya: Ko matatar Dangoto za ta taimaka?

To sai dai kuma sabon rikicin na kara fitowa fili fa kila kama karyar ma‘aikata a kasuwar Najeriya. Rikicin na Dangote da ke zaman kamfani mafi girma a kasar dai na iya aiken sakon bababkere na kodagon cikin harkokin kasuwar Najeriya.

To sai dai kuma ciki da gaskiya, a tunanin Ibrahim Shehu da ke zaman sakatare na kungiyar dillallan mai ta kasar, yana ganin ciki da gaskiya wuka ba ta huda shi. Duk da sallamar 800 din dai ,har ya zuwa yanzun dai sama da mutane 3,000 ne dai ke aiki a matatar ta Dangote.

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani