Amurka ta musanta batun harbin jirgin yakinta a Hormuz
May 4, 2026
Kamfanin dallancin labaran Iran Fars, ya ruwaito cewa sojojin juyin juya halin Musulumcin kasar sun harba makamai masu linzami guda biyu kan wani jirgin ruwan yakin sojin Amurka a mashigar Hormuz, wanda Teheran da Washington ke takaddama kan tsoshe zirga-zirga ta cikin sa tun bayan barkewar yaki a ranar 28 ga watan Fabarairu.
Majiyar ta ce lamarin ya faru a ranar Litinin a kusa da tashar jiragen ruwan Iran ta Jask, bayan da jirgin ruwan yakin na Amurka ya keta dokokin zirga-zirgar Teku tare kuma da bijire wa gargadi da sojoji suka yi masa.
Sai dai tuni rundunar sojin Amurka da ke yankin Gabas ta Tsakiya ta karyata wannan labari a cikin wani sako da ta wallafa a shafinta na X.
Amurka za ta fara rakiyar jiragen ruwa a mashigin Hormuz
Wannan dai na zuwa ne kawana guda bayan da shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da kaddamar da aikin ba da kariya da rakiya ga jiragen ruwa na 'yan kasuwa da ke wucewa ta mashigin Hormuz domin samar da sa'ida ga harkokin kasuwanci a duniya.