1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Amurka ta sake yin fatali da kiran tsagaita bude wuta a Gaza

Binta Aliyu Zurmi
September 19, 2025

Amurka wacce ta dare a kujerar naki ta dakile kiran da kwamitin sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya yi na tsagaita bude wuta a Gaza cikin gaggawa ba tare da wani sharadi ba.

https://p.dw.com/p/50j1Q
UN-Sicherheitsrat New York 2025 | Sitzung zur Lage in Gaza und Abstimmung über Waffenruhe
Hoto: Angela Weiss/AFP/Getty Images

Mambobin kwamitin 14 sun goyi bayan kudurin wanda aka gabatar tun a watan Augusta a matsayin mayar da martani ga sanarwar da Majalisar Dinkin Duniya ta yi na matsananciyar yunwa da al'ummar Gaza ke fama da ita.

Zaben ya zo ne a dai-dai lokacin da tankunan yaki da jiragen yakin Isra'ila ke ci gaba da yin luguden wuta Gaza, inda kuma ake shirin kai wani sabon farmaki ta kasa, lamarin da ya tilastawa dubban Falasdinawa tserewa daga gidajensu.

Kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya ce kudirin ya bukaci tsagaita bude wuta na didindin cikin gaggawa ba tare da sharadi ba  a Gaza wanda aka bukaci dukkanin bangarorin su mutunta shi gami da sakon 'yan Isra'ila nan ma ba tare da wani sharadi ba.

Amurka ta sha yin watsi da irin wannan bukata, wanda ko a watan Yunin da ya gabata ta yi amfani da karfin kujerarta ta na din-din-din  wajen marawa Isra'ila baya.

Karin Bayani: Majalisar Dinkin Duniya ta goyi bayan kafa kasar Falasdinu