1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Sabon farmakin Isra'ila kan Gaza

Suleiman Babayo MAB
September 16, 2025

Dakarun Isra'ila sun kaddamar da sabon farmaki a yankin zirin Gaza na Falasdinu domin ganin bayan tsagerun kungiyar Hamas masu dauke da makamai, amma matakin ya fuskanci suka daga wasu kasashen duniya.

https://p.dw.com/p/50a8a
Dakarun Isra'ila
Dakarun Isra'ilaHoto: Menahem Kahana/AFP/Getty Images

Dakarun Isra'ila sun kaddamar da sabon farmaki a yankin zirin Gaza na Falasdinu, inda dakarun ke cewa za su zurfafafa dannawa cikin yankin domin tunkarar mayakan kungiyar Hamas kimanin 3,000. Akwai masu tababa da nuna dari-dari da haka a cikin Isra'ila kan makomar 'yan Isra'ila da aka yi garkuwa da su a cikin yankin na Falasdinu.

Rkiicin ya fadada

Dakarun Isra'ila
Dakarun Isra'ilaHoto: Israel Defense Forces/Xinhua News Agency/picture alliance

Farmaki na zuwa lokacin da kasashen Turai ke barazanar takunkumin kan gwamnatin Isra'ila.

Shi ma sakatare janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antonio Guterres ya ce matakin na Isra'ila kan yankin na Falasdinu ya saba ka'idojin siyasa da dokokin duniya.

Sannan babban jami'in na majalisar Dinkin Duniya ya ce yana shirye da ganawa da Firaminista Benjamin Netanyahu na Isra'ila da Shugaba Donald Trump na Amurka, lokacin taron majalisra a mako mai zuwa.