1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaAfirka

Ana zaman zullumin siyasa a Tanzaniya

Suleiman Babayo AH
December 9, 2025

Ana zaman zullumi kan zanga-zanga da aka shirya a kasar Tanzaniya.

https://p.dw.com/p/55215
Mutane sun watse a binrin Dar es Salaam na Tanzaniya
Mutane sun watse a binrin Dar es Salaam na TanzaniyaHoto: AFP/Getty Images

A birnin Dar es Salaam cibiyar kasuwancin kasar Tanzaniya ya kasance fayau ba kowa, bayan jami'an tsaro sun mamaye birnin bayan shirya zanga-zanga nuna adawa da gwamnati, biyo bayan tashe-tahsen hankula lokacin zaben kasar.

Yanayin da ake ciki

Mutane sun watse a binrin Dar es Salaam na Tanzaniya
Mutane sun watse a binrin Dar es Salaam na TanzaniyaHoto: Eric Boniface/DW

Tun farko Firaminista Mwigulu Nchemba ya bukaci mutane su zauna a gida domin guje wa rikicin da zai iya tashi sakamakon zanga-zangar da aka shirya.

A makon jiya 'yan sanda suka suka haramta duk wata zanga-zanga biyo bayan tashe-tahsen hankula na zabukan watan Oktoba da ya gabata, inda Shugaba Samia Suluhu Hassan ta lashe zaben da kaso 98 cikin 100 na kuri'un da aka kada.

'Yan adawa sun ce fiye da mutane 1,000 suka halaka sakamakon rikicin zaben kasar ta Tanzaniya.