1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaGabas ta Tsakiya

Yaki ya barke a mashigin Hormuz

Mahmud Yaya Azare AH
May 5, 2026

Kwana guda bayan da Shugaban Amurka Donald Trump ya kaddamar da shirinsa na ceto jiragen kasuwancin da suka makale a mashigin Hormuz, artabu ya barke tsakanin kasashen biyu.

https://p.dw.com/p/5DJj3
Mashigin Hormuz
Mashigin HormuzHoto: Amirhosein Khorgooi/ISNA/AP Photo/picture alliance

Babbar manufar wannan shiri na sojin  Amurkadai shi ne buɗa MashiginHormuz ta hanyar riƙa yi wa manyan jiragen dakon kaya rakiya. Rundunar sojin Amurkan ta tsara cimma muradin nata ne kuma ta hanyar girke dakaru aƙalla dubu 15,000, da jiragen yaƙin ruwa da za su share nakiyoyin da Iran ta dasa a mashigin ruwan na Hormuz.

Kamfanin dakon kaya ta ruwan teku Maersk ya sanar da cewa daya daga cikin jiragensa sun fice daga mashigin ruwa na Hormuz da sanyin  karkashin kulawa da rakiyar sojojin Amurka. Sai dai gidan TV kasar ta Iran ya musunta wannan ikirarin:

Mashigin Hormuz
Mashigin HormuzHoto: Amirhosein Khorgooi/ISNA/AP Photo/picture alliance

“Ofishin Khatamul Anbiya na rundunar huyin huya hali na tabbatar da cewa, mashigin Hormuz na karkashin kulawar dakarunsa,har kuma ya zuwa babu hirgi ko guda daya ratsa shi ba tare da izininsa ba.Ya kuma yi nasarar lalata yunkurin yin rakiya ga wasu jirage dajiragen makiya suka yi kokarin yi.Yana mai gargadin sauran jirage da su guji yin hakan don kaucewa hatsarin da zasu jefa kansu cikinsa.”

Shugaba Trump din dai ya ce babu gudu ba ja da baya kan aiwatar da shirin yenta jiragen ruwan kimanin dubu da ke makale a mashigin na Hormuz,yana mai barazanar share Iran daga doron kasa idan ta kuskura ta kai hare-hare kan jiragen ruwansa.

Lendesy Agraham,dan majalisar dattijan Amurka ne da ke goyan bayan wajibcin kwace iko da mashigin na Hormuz koda hakan zai kawo ga komawa yaki ruwa:

Mashigin Hormuz
Mashigin HormuzHoto: Amirhosein Khorgooi/ISNA/AP Photo/picture alliance

“Batun kwace ikonmu da mashigin  Hormuz ta faru ta kare. Dole ne mu yi hakan koda yarjejeniyar tsagaita wuta zata rushe yaki ya koma ruwa ne. Domin wannan mashigin shi ne makamin daya tilo daya ragewa Iran takewa duniya barazana da shi. Da mun gama kwace shi ,ta faru ta kare,an yiwa mai dami daya sata.”

To sai dai Ministan harkokin wajen Iran, Abbas Araghchi ya ce abubuwan da suka faru a Mashigar Hormuz na nuni da cewa matakan soji ba za su iya warware abin da ya kira rikicin siyasa ba, yayin da ake fargabar sake ɓarkewar yaƙi tsakanin kasarsa da Amurka.

Araghchi ya kuma gargaɗi Amurka kan ta yi taka tsan-tsan, kuma kar ta bari masu mummunan fata su sake jefa ta cikin yaƙi.

Mashigin Hormuz
Mashigin HormuzHoto: Amirhosein Khorgooi/ISNA/AP Photo/picture alliance

A hannu guda,shugaban   gamayyarjiragen kungiyar dakwo kan Teku,Jeremy Dowen ya gargadi matuka jiragen da su guji biye wa shirin shugaba Trump na yunkurin yentansu.