Ayyukan gwamnati sun tsaya cik a Amurka
October 1, 2025
Gwamnatin Amurka ta rufe yawancin ayyukanta a ranar Laraba bayan sabani mai tsanani ya hana Majalisar Dokoki da Fadar White House cimma matsaya kan kudi da ya kamata a kashe.
Tsaikon zai hana fitar da rahoton aikin watan Satumba da jinkirta zirga-zirgar jiragen sama da dakatar da binciken kimiyya da hana sojojin Amurka albashi, tare da tilasta wa ma'aikatan tarayya 750,000 shiga hutun dole da kuma asarar kusan dalar Amurka miliyan 400 a kullum.
Majalisar dokokin Amurka ta amince da dokar kasafin kudin Trump
An shiga wannan rudanin ne sa'o'i bayan Majalisar Dattawa ta ki amincewa da kudirin kashe kudi na wucin gadi da zai ci gaba da tafiyar da harkokin gwamnati har zuwa 21 ga watan Nuwamba.
Trump, wanda yakin neman zaben sa na sake fasalin gwamnatin tarayya ya rigaya ya sanya kimanin ma'aikata 300,000 cikin shirin barin aiki nan da watan Disamba, ya gargadi 'yan jam'iyyar Democrat a majalisa cewa dakatarwar za ta janyo matsaloli da ba za a iya magance lahanin da za su haddasa ba saboda zai kori ma'aikata.
An rufe hukumomin gwamnati a Amurka
Ya zuwa yanzu babu wata hanya da aka ga alamar za ta kawo karshen wannan tsaikon, yayin da hukumomi suka yi gargadi cewa wannan shi ne karo na 15 da harkokin gwamnatin suka tsaya cik tun daga 1981 a Amurka.