SiyasaAfirka
Bukukuwan Sallah a Nijar tare da Tiani
March 19, 2026
Talla
An dai karfafa tsaro tun a jajibirin sallah shugaban kasa Abdourahamane Tiani ya halarci Sallar Idi tare da sauran manyan jami'an gwamnati da ma tsoffin shugabannin kasa irin su Mahamane Ousmane da Mahamadou Issoufou inda aka yi aka kammala cikin tsatsauran mataki na tsaro.
A halin yanzu dai za a iya cewar sallah ta zo ne a daidai lokacin da kasar ta Nijar da ma yankin Sahel na AES ke fuskantar tarin matsaloli na tsaro duk kuwa da jajircewar da jami'an tsaron wadannan kasashe ke yi, inda a Nijar kungiyoytin fararan hula suka kira tarukan gangami bayan kammala shagulgullan sallah domin sa ido da kara fadakarwa kan harkokin tsaro.