1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaBrazil

Bolsonaro ya daukaka kara kan daurin shekaru 27

October 28, 2025

Kotu ta samu tsohon shugaban Brazil Jair Bolsonaro da laifin yunkurin juyin mulki, zargin da tsohon shugaban ke ci gaba musantawa.

https://p.dw.com/p/52fzN
Tsohon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro a gidansa na Brasilia a cikin daurin talala
Tsohon shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro a gidansa na Brasilia a cikin daurin talalaHoto: Sergio Lima/AFP

Lauyoyin Bolsonaro sun daukaka kara kan hukuncin daurin shekaru 27 da kotu ta yanke masa sakamakon zargin jagorantar hambarar da gwamnatin Luiz Inacio Lula da Silva, biyo bayan faduwa zaben 2022.

Karin bayani:Kotu ta samu Bolsanaro da laifin yunkurin juyin mulki

A watan Satumbar 2025, wasu lauyoyi biyar daga kotun kolin kasar sun samu Bolsonaro da laifin yunkurin juyin mulki tare da wasu laifukan guda biyar da suka hada da yi wa dimokuradiyya karan-tsaye.

Karin bayani:Tsohon shugaban Brazil Bolsonaro ya musanta yin juyin mulki

Masu gabatar da karar sun ce juyin mulkin bai yi nasara ba sakamakon rashin hadin kai daga wajen sojoji. Tsohon shugaban da ya mulki Brazil daga 2019 zuwa 2022 na ci gaba da fuskantar daurin talala a cikin gidansa kafin kotu ta kammala tantance takardun karar da aka shigar domin kai shi gidan wakafi ko kuma wanke shi daga zargin da ake masa.