SiyasaAfirka
CAF ta dakatar da kocin Senegal shiga gasar wasanni
January 29, 2026
Talla
A wata sanarwa da hukumar ta fitar, ta bayyana cewa ta samu Pape Thiaw da laifin rashin dattako, a yayin wasan karshe da Senegal ta lallasa Maroko da ci 1-0, a ranar 18 ga watan Janairu. An kuma dakatar da shi shiga gasar wasanni biyar. CAF ta kuma haramta wa 'yan wasan Senegal da ke taka leda a Firimiyar Ingila, Iliman Ndiaye da Ismaila Sarr, shiga gasar wasanni biyu. An kuma ci tarar Hukumar Kwallon Kafa ta Senegal Dala $615,000.
Karin bayani:Senegal: Lashe gasar AFCON cikin Labarin Wasanni
Daga bangaren Moroko kuwa, CAF ta dakatar da 'dan wasan gaba na kasar, Ismael Saibari, shiga wasanni uku da kuma tarar Dala $100,000, haka kuma an dakatar da kyaftin din Moroko Achraf Hakimi shiga wasanni biyu.