CDU da SPD za su koma tattaunawa don kafa gwamnati a Jamus
March 3, 2025
A ranar Litinin ne bangaren jagoran jam'iyyar CDU Friedrich Merz da kuma na shugabannin jam'iyyar SPD za su koma teburin tattaunawa domin duba yiwuwar samar da hadaka ta sabuwar gwamnatin Jamus.
A ranar Juma'a ce aka fara tattaunawar tsakanin bangarorin biyu kuma a yanzu an koma tattaunawar ce da gaggawa bayan cacar baka da ta kaure tsakanin shuagban Amurka Donald Trump da kuma na Ukraine Volodymyr Zelensky a fadar White House a ranar Juma'a.
Ya ya kawancen kafa gwamnatin Jamus zai kasance?
Lamarin da ya faru ya sa wasu kasashen Turai fara ganin Amurka a matsayin kasar da babu tabbbas kanta a kan sha'anin kawancen tsaro.
Bayan nasarar da ta samu, jam'iyyar CDU/CSU na neman yadda jagoranta Friedrich Merz zai maye gurbin Olaf Scholz a matsayin sabon shugaban gwamnatin Jamus.
Jam'iyyar CDU/CSU na kan gaba a zaben Jamus
Jam'iyyar ta Scholz SPD ita ce ta zo ta uku bayan CDU da AfD sun zo a matsayin ta daya da ta biyu.