Rasha: Sabon takunkumi daga Tarayyar Turai?
February 6, 2026
Matakan da Hukumar Zartaswar kungiyar Tarayyar Turan ke shirin dauka sun hadar da daina taimakon jiragen ruwan dakon man Rasha wajen kula da lafiyarsu da kara matse bangaren tattalin arzikin kasar da hada-hadar cinikyayya da sauran kasashen duniya.
Ranar Litinin din mako mai zuwa, ake sa ran kasashen na kungiyar Tarayyar Turai za su tattauna matakin a hukumance. Shugabar Hukumar Tarayyar Turan Ursula von der Leyen ta ce duk da ana tattaunawa domin kawo karshen yakin, tilas sai da matsin lamba kafin Rasha ta mika wuya wajen tattaunawa da zuciya guda.
Kusan daukacin mambobin kungiyar kasashen Turan sun amince da shirin na hana kula da jiragen ruwan da suke dakon man-fetur daga Rasha, inda haka zai kara kassara yawan man fetur din da Moscow ke fitarwa zuwa kasashen ketere.