1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Faransa ta goyi bayan Spain bayan matakin harajin Trump

March 4, 2026

Bayan ayyana matakin karin harajin kasuwanci da gwamnatin Amurka ta yi a kan Spain saboda rashin goyon baya kan yakin Iran, Faransa ta ce tana tare da kasar ta Spain a halin da ake ciki.

https://p.dw.com/p/59nCD
Shugaba Emmenuel Macron na Faransa
Shugaba Emmenuel Macron na FaransaHoto: John Thys/AFP

Shugaban Faransa Emmanuel Macron ya bayyana goyon bayansa ga shugaban Spain Pedro Sanchez bayan da ya fuskanci barazanar karin kudin haraji na cinikayya a tsakanin kasashen biyu.

A jiya ne Shugaba Trump ya fadi cewar zai dauki matakin da ya cancanta a tsakanin Amurka da Spain saboda rashin goyon bayan da gwamnatin kasar ta nuna kan yakin Iran, yana mai bayyana cewar matakin da Spain ta dauka ba ya da muhimmanci.

Ko a jiya Talata ma dai sai da shugaban na Faransa Emmaneul Macron ya tabbatar da sabon shirin gwamnatin kasar na inganta makamin Nukiliya a wani yunkuri na kare kan kasa daga duk wata barazana.