Trump ya sanya harajin kashi 25 ga abokanan kasuwancin Iran
January 13, 2026
Shugaban Amurka Donald Trump ya lafta wa kasashen da ke huldar kasuwanci da Iran harajin kashi 25 cikin 100, a daidai lokacin da ake ci gaba da zanga-zangar kawo karshen gwamnatin Jamhuriyar Islama ta Iran da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane akalla 648.
Karin bayani:EU ta haramtawa jami'an gwamnatin Iran shiga kasashenta
Matakin Trump dai zai shafi kasashen da ke gudanar da kasuwanci da Iran da suka hada da China da Turkiyya da Hadaddiyar Daular Larabawa da kuma Iraqi.
Karin bayani:Zanga-zangar Iran: Trump na tunanin daukar matakin soji
Kungiyar Tarayyar Turai ta jaddada goyon bayanta ga masu zanza-zangar, tare da shan alwashin sanya sabbin takunkuman karayar tattalin arziki kan Iran. A gefe guda, Hukumar Gudanarwar Tarayyar Turai ta kori dukkan jami'an diflomasiyyar Iran da ke wakiltar kasar a EU.