EU ta haramtawa jami'an gwamnatin Iran shiga kasashenta
January 12, 2026
Majalisar tarayyar Turai ta sanar da haramtawa jami'an diflomasiyyar Iran da ma na gwamnati shiga kasashenta, sakamakon zarginta da amfani da karfi fiye da kima a kan masu zanga-zangar adawa da tsadar rayuwa a kasar.
Shugabar majalisar Roberta Metsola, ta ce Turai ba za ta taba aminta da yadda gwamnatin Iran ke gallazawa al'ummarta ba, har ma da kashe wasunsu, kamar yadda ta wallafa a shafinta na sada zumunta na X ranar Litinin.
Karin bayani: Zanga-zangar Iran: Trump na tunanin daukar matakin soji
Daruruwan mutane ne suka rasa rayukansu a yayin wannan zanga-zanga, wadda aka fara a ranar 28 ga Disamban shekarar da ta gabata ta 2025.
Ko a ranar Lahadi sai da Roberta Metsola ta shawarci mahukuntan Iran su sauya salon yadda suke tunkarar masu boren, domin daina kashe su.