Fina-finan Indiya na kara tsamin alaka da Pakistan
January 14, 2026
Batu da ya jima yana janyo muhawara da rura wutar gaba tsakanin Indiya da makwabciyarta Pakistan, bai wuce yadda sau tari mashirya fina-finan ke karkata jigon labarin fim ga alkiblar nuna Pakistan a matsayin kasa mai kyankyashe ‘yan tarzoma, ko kuma goyon ta'addanci ba. Wannan bakin tambari yana fusata al'ummar Pakistan da ma wasu kasashen duniya da ke da sabanin fahimtar addini da Indiyawa.
Karin bayani: Dharmendra: Babban bango ya fadi a Bollywood
Wani sa'in ma munin lamarin ya kan kai ga haramta nuna fina-finan Indiya a cikin kasar Pakistan da sauran aminanta, alal misali fim Dhurandhar" da ya fito a cikin watan Disamban 2025. Wannan fim, an gina labarinsa a kan ayyukan leken asiri da yaki da ta'addanci, tare da nuna yadda kwararrun jami'an tsaron indiya suka tarwatsa maboyar 'yan ta'adda a Pakistan.
Yawan fina-finai da ke zambo ga Pakistan
Fina-finan Bollywood irin wadannan sun fi tarin shurin masaki da madubinsu ke haska Pakistan a matsayin babbar abokiyar gaba mai shirya tuggun muggan hare-haren ta'addanci ga Indiya, bisa turbar addini, musamman kan yankin Kashmir, wanda kasashen biyu ke takaddamar ikonsa yau kusan shekaru 80, inda suke tallata manufofin jam'iyyar BJP mai mulkin kasar, har ake saka musu da tukuicin janye musu haraji.
"Gabar da ke tsakanin Indiya da Pakistan bayan raba kasashen kusan shekaru 70 na nan, duk waata hanyar da Indiya za ta bi don musanta wa Pakistan ta fuskar addini sai ta yi, saboda Pakistan ta zabi musulunci, su kuma Indiya suna bauta wa gumawa duk da da cewa akwai musulmai." Inji kwararre a fannin ilimi da aikin jarida da al'adu, Farfesa Abdallah Uba Adamu.
Farfesa Abdalla ya kara da cewa "Duk finaf-finan da ake yi na yake-yake a kasashe kamar Afganistan da Iraki duk yada farfaganda ce, kuma babu wanda ke magana a kansu" Abin da ya sa aka fi ganin na Indiya da Pakistan ya fi kamari shi ne, Indiya da Pakistan duk daya suke, addini ne ya raba su.
Bukatar kaffa-kaffa a Bollywood
Sai dai, ganin baiken mashirya fina-finan bai tsaya a Pakistan ba, domin har a cikin gida an samu hakan, alal misali Ishita Sengupta, wata ‘yar jarida kuma mai rubuce-rubuce da sharhi kan fina-finan Indiya, ta ce " Ya kamata masu shirya fina-finan su rinka yin taka tsan-tsan a cikin sha'anin addinai da al'adu, la'akari da dimbin mabiya addinai daban-daban da kasar ke da su."
Karin bayani: Yaushe za a ga 3 Khans a fim daya?
Haka ma batun yake ga fitacciyar lauya a kotun kolin Indiya Shahrukh Alam, inda ta ke cewa "Lalaci ne da son cin bbanza ke sa wasu ‘yan Bollywood fitar da fina-finain da ke tallata farfagandar gwamnatin Indiya, don kawai cin moriyar janye musu haraji, ba tare da la'akari da mummunan tasirin fim din ba, wanda ke kara cusa kiyayya da gaba da tsoro da ma fargaba a tsakanin al'umma."
Duk da cewa gwamnatin Indiya ba ta tallafa wa masana'antar da kudi kai tsaye a hukumance, amma ana ganin kusoshin jam'iyyar BJP ciki har da Firaiminista Narendra Modi na tallata wasu fina-finai, da kuma kyakkyawar alakar wasu manyan jarumai da gwamnatin na taiamakawa wajen yada farfagandar siyasa ko addini. Amma jam'iyyar BJP mai mulkin Indiya ta musanta zargin cusa kiyayyar wata kasa ko addini ko al'adun da suka saba da manufofinta a cikin fina-finan Bollywood, tana mai cewar "Babu abin da ake nuna wa face jarumtakar al'ummar Indiya"
Hanyar dinke barakar Indiya da Pakistan
Mai magana da yawun jam'iyyar ta kasa Shazia Ilmi, ta ce "Ko a masana'antar Hollywood ta Amurka, an ga manyan fina-finan duniya da suka nuna wasu kasashe a matsayin makiyansu, misali da 'yan kasar Rasha Ivan Drago a cikin fim din Rocky IV, sai Ivan Vanko a cikin Iron Man 2, da Viggo Tarasov a cikin John Wick, da Yuri Komarov a fim na "A Good Day to Die Hard", da ma Lt. Col. Sergei Podovsky a shahararren fin din nan Rambo."
Karin bayani: Yankin Gulf na narka kudi a Hollywood don kare martaba
Shazia Ilmi ta kara da cewa "Akwai alamun fuska biyu a bangaren masu sukar kasarta, kasancewar yadda kasashen ke yin na su fina-finai cikin tallata karfin ikon sojojinsu da nasararonsu karara, amma a gefe guda ake sukar Indiya, don kawai ta yi nunin samun galaba a kan magauta."
Farfesa Abdallah Uba Adamu ya ce shi fim kasuwanci ne, babu ruwanci da abin da zai biyo baya "Idan da mutane ba su son irin fina-finan da ba za su saya ba." Babu wanda ya kai kasar Indiya yin fim na nuna al'adu.