1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Hanyar neman tsagaita wuta a Ukraine

Suleiman Babayo ATB
December 26, 2025

Shugaban Ukraine zai gana da na Amurka nan gaba kan samar da zaman lafiya tsakanin Ukraine da Rasha.

https://p.dw.com/p/55zkC
Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine
Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar UkraineHoto: Ukrainian Presidential Office/AFP

Shugaba Volodymyr Zelensky na kasar Ukraine a wannan Jumma'a ya ce nan gaba kadan zai gana da Shugaba Donald Trump na Amurka, kan matakan neman kawo karshen kutsen Rasha kan kasarsa.

Tattaunawar neman kawo karshen yakin

Yakin Rasha da Ukraine
Yakin Rasha da UkraineHoto: via REUTERS

Wannan na zuwa bayan ganawa tsakanin wakilan kasashen biyu na Ukraine da Amurka, inda suka tattauna muhimman batutuwa na kawo karshen yakin da ke faruwa tsakanin Ukraine da Rasha.

Mahukuntan Rasha sun nuna alamun amince da kudirorin na tsagaita wuta.

A wani labarin Mataimakin Firamnistan Rasha, Denis Manturov ya ce kasar tana ci gaba da jinkirta fitar da makamai zuwa kasashen ketere domin ganin ta samar wa kanta abin da take bukata a yankin da ke faruwa tsakanin kasar da Ukraine.